✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mun saya wa ’yan banga kayan aikin N500m –Gwamnatin Neja

Gwamnatin ta sanya na'urar CCTV a kananan hukumomi 25 da ke jihar don inganta sha'anin tsaro.

Gwamnatin Neja ta ce ta kashe Naira miliyan 500 wajen saya wa ’yan banga kayan aiki domin inganta tsaro a jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Emmanuel Umaru, ya ce kayan aikin da aka samar sun hada da kyamarar tsaro ta CCTV da aka dasa a kananan hukumomi 25 a jihar.

Da yake bayani a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dokokin jihar a ranar Laraba, ya ce gwamnatin jihar ta yi gagarumin aiki wajen samar da kayan aikin da suka dace ga jami’an tsaro kuma za ta yi duk mai yiwuwa don ganin tsaro ya inganta a fadin jihar.

A nasa jawabin, shugaban kwamitin, Jibrin Baba, mai wakiltar Mazabar Lavun, ya ce dalilin zaman nasu shi ne yin duba da kudaden da aka ware wa ma’aikatar a kasafin 2023.

Ya ce sun gayyaci kwamishinan ne don ya yi musu bayanin yadda ma’aikatar za ta kashe kudaden a matsayinta na sabuwar ma’aikata da aka kafa a jihar.

Neja na daga cikin jihohin Arewa da ke fama da hare-haren ’yan bindiga.

Hare-haren ’yan bindigar sun yi sanadin salwantar rayukan dubban mutane, tare sa sanya wasu da yawa zama ’yan gudun hijira.