✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kasa samun natsuwa tunda muka sace Sarkin Kajuru — ’Yan bindiga

Sarkin na sane da shirin sace shi.

’Yan bindigar da suka sace Sarkin Kajuru da ke Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna, Alhaji Alhassan Adamu sun ce sun kasa samun natsuwa tun da suka sace Sarkin.

’Yan bindigar sun sako Sarkin ne kwana daya da sace shi tare da wadansu mutum 13, bayan a farko sun bukaci a ba su Naira miliyan 200 kudin fansa.

Sai dai daya daga cikin makusantan Sarkin ya ce ’yan bindigar sun nemi afuwa kan sace Sarkin da suka yi kafin su mika shi ga wadanda suka je karbo shi.

Majiyar Aminiya wadda take cikin wadanda suka je suka tarbo Sarkin ta ce ’yan bindigar ne suka kira su ta wayar Sarkin da yamma, suka shirya tarbar Sarkin.

Majiyar ta ce da suka je karbo Sarkin a kusa da garin Gengere, ’yan bindiga uku rike da makamai sanye da kayan sojoji suka kawo musu shi, sannan suka nemi a yafe musu.

“Abin mamaki ya ba mu, sai muka tsaya muna kallon su a lokacin da suke neman afuwar.

Sun ce ba su samu natsuwa ba tun sace Mai martabar da suka yi.

“Suka umarci mu tafi da shi gida amma za a ci gaba da tattauna makomar sauran mutum 13 da suke hannunsu,” inji majiyar.

A ranar Lahadin da ta gabatace ’yan bindigar suka kutsa gidan Sarkin, suka dauke shi tare da iyalansa 13.

Garin Kajuru yana da nisan kilomita 37 ne daga garin Kaduna a hanyar zuwa Kachiya, kuma yana kusa da mahadar Karamar Hukumar Chikun ce, inda aka sace dalibai 121 a makarantar kwana a ranar Litinin din makon jiya.

Wakilinmu wanda ya ziyarci garin ya gano cewa ’yan bindigar sai da suka kewaye inda sojoji suke zama a gaban Kwalejin GSS Kajuru kafin su yi aika-aikarsu.

Yadda suka shigo gidanmu – Matar Sarkin

Matar Mai martaba Sarkin Kajuru, Hajiya Hadiza Alhassan ta ce bayan sun karya kofar gidan, sai suka tsaya a bayana wai sai na fada musu inda Sarki yake. “Sun zo da manyan makamai da kayan sojoji a jikinsu.

Na fada musu Sarki ba ya nan, Daya daga cikinsu ya ce zan yi bayani in suka kama shi, sauransu kuma suna ta bincike a cikin dakuna.

“Bayan sun yi nasara sun balle kofar ce suka yi saurin shiga dakin. Sun fito da Sarkin waje inda suka tambaye shi ko shi ne Sarkin, sai ya ce musu shi ne, sai suka tafi da shi,” inji ta.

Wadanda aka sace

Matar Sarkin ta ce suna zaune da Sarkin da ’yarsa mai shekara 25, Zainab Alhassan da jikarsa mai shekara 15, Zainab Mukhtar da sauran jikokinsa hudu; Muhammad Sa’adanu Musa da Salim Musa da Faisal Musa da Ahmad Mukhtar lokacin da abin da ya faru.

Daga cikin wadanda aka sace akwai Sulaiman Umar wato Sallaman Sarki.

Sauran ’yan uwan Sarkin da aka sace sun hada da Nazifi Rayyanu da Ayuba Yunusa da Amina Abubakar da Maryam Abubakar da Mardiya Sani da danta mai shekara daya Mudassir Sani.

A taron da Masarautar Kajuru ta yi da manema labarai, wanda Galadiman Kajuru Alhaji Dahiru Abubakar ya jagoranta, ta ce ’yan bindigar sun zo ne da yawa suka tare duk wata hanya ta shiga da fita garin.

Mutum 10 aka sace – ’Yan sanda

A bayanin da Rundunar ’Yan sandan Kaduna suka fitar na tabbatar da faruwar lamarin, ta ce mutu 10 aka sace.

Kakakin ’yan sandan, ASP Jalige Muhammad ya ce hadin gwiwar ’yan sanda da sojoji da suke Kajuru suna ci gaba da aikin ceto wadanda aka sace.

‘Sarkin na sane da shirin sace shi’

Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu yana da masaniyar abin da zai faru, don har ya fada wa jami’an tsaro sa’o’i 48 kafin faruwar harin.

Wata majiyar masarautar ta bayyana cewa, Sarkin mai shekara 85 wanda ya hau karagar sarauta a 1978, ya zauna da jami’an tsaro a ranar Juma’a da rana ya sanar da su shirin sace shi da ake yi, kuma sai aka sace shi a ranar Lahadi.

Muna zaman dar-dar

Mutanen Kajuru Mazauna garin Kajuru sunbayyana rashin jin dadinsu a kan sace-sacen da suke faruwa da kuma sace Sarkin Kajuru da mutum 13 da aka yi.

Sun ce jami’an tsaro sun isa gidan Sarkin ne da misalin karfe 4 na Asuba bayan ’yan bindigar sun tafi.

Shamsu Isa wanda ya kubuta daga hannun ’yan bindigar ya ce matasa sun fada wa jami’an tsaron su tafi ba sa bukatarsu.

Muhammad Shu’aibu wani mazaunin Kajuru ya ce ya sha da kyar ne ta hanyar hawa katanga lokacin da ’yan bindigar suka zo kusa da gidansa.

Sannan ya buya a karkashin mota, ya kira sojojin da aka sa a garin, sojin sun ce masa su ma ’yan bindigar sun zagaye su.

Muhammad Dan’asabe kafinta da aka taba sace shi, ya biya Naira miliyan daya, ya ce sace Sarkin laifi ne babba.