A Majami’ar ECWA ta 1 da ke Unguwar Bolari, Sakataren Majami’ar, Jerome Jeremiah wanda ya yi magana a madadin Fastonsu cewa ya yi su fi shekara 20 suna yin gwaje-gwaje kafin daura aure, kuma ba na kanjamau kadai ba har da na sikila da ciki da rukunin jini da sauransu:
A majami’arku kafin a daura aure ana yin gwaji ne?
A darikarmu ta ECWA muna tura ma’aurata Asibitin kwararru na Jiha wata shida kafin aure su je a yi musu gwaji, kuma ba su za su kai kansu ba, majami’a ce za ta tura su idan aka yi gwajin kuma karbo sakamakon za a yi ba su za su karbo da kansu ba.
Iya na kanjamau kuke yi ko har da na sauran gwaje-gwajen?
Duk wani gwaji da ka sani ana yi, hatta gwajin kwayar halitta don gane ko za su iya haihuwa idan suka yi aure, domin kada idan an yi aure shekara daya ko biyu ba haihuwa a fara samun sabani.
Ka ce ku kuke tura masu niyyar auren asibiti me ya sa?
Eh, mu muke tura su amma kafin nan suna zuwa da kansu su gwada su san matsayinsu shi ya sa idan suka je asibitin ba a samun matsala saboda kowa ya san kansa.
Wace shawara kuke ba su?
Shi ya sa idan aka zo lokacin daurin aure ma ba a samun kowace matsala saboda yadda muke ba su shawarwarin da suka dace tun farko.