✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun amince a haramta yawon kiwo —Dattawan Arewa

Kungiyar ACF ta bukaci gwamnonin Arewa su amince a haramta yawon kiwo a jihohinsu.

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta goyi bayan gwamnonin Kudu 17 kan haramta yawon kiwo a Najeriya.

Shugaban ACF, Cif Audu Ogbeh, ya ce dattawan ba su da ja tun da gwamnonin Kudun sun yanke shawarar ne da kyakkyawar manufa ta kare dukiyoyin manoma.

Ogbeh ya ce: “Gaskiya, rikicin manoma da makiyaya ya samo asali ne daga tunanin yawancin makiyaya na cewa suna da ’yancin shiga kowace gona, su ci amfanin gona, su yi fyade ko su kashe duk wani da ke nuna adawa. Babu wani mutum ko wata al’umma da za ta yarda da hakan.

“Tashin gwauron zabon farashin gari rogo a halin yanzu daya ne daga cikin illolin wannan halayyar.

“Wasu gonakin rogo ma ba a bari su girma har a manoman su girbe, wanda hakan kuma barazana ce ga samar da abinci.”

Ya kamata gwamnonin Arewa su amince

Audu Ogbeh ya kara da kira ga gwamnonin da su dage wajen haramta kiwo a fili bisa amannar cewa hakan zai kawo karshen rikici tsakanin makiyaya da manoma.

A cewarsa, yawancin makiyayan da ke tayar da rikici ’yan kasashen waje ne “da ke dandazo suna shigowa daga kasashen Afirka makwabta, ba tare da mutunta iyakoki na jiha ko na yanki ba. Saboda haka dole ne a taka musu burki.”

“Saboda haka, ya zama wajibi a bi shawarar Gwamnan Umar Abdullahi Ganduje na hana shigowar makiyaya Najeriya daga kasashen Afirka ta Yamma.

A haramta bakin makiyaya shigowa

“Wata mafitar kuma ita ce Najeriya a yi kwaskwarima ga sashe na 3 na yarjejeniyar ECOWAS, game da zirga-zirgar shanu da sauran dabbobi ba tare da samun izini na musamman ba.

“Idan aka yi haka, muna da sama da hekta miliyan 5 na tsoffin wuraren kiwo, da za mu iya daukar shanu sama da miliyan 40 idan suna da ciyawa da ruwa.

“Ya kamata gwamnonin Arewa su gaggauta duba wannan su ga yiwuwar hakan.

“A cikin wadannan wuraren, ana iya samar da wuraren kiwo don ba da haya ga makiyaya don a kawo karshen wannan lamarin. Daga nan kuma ana iya hukunta duk makiyayin da aka samu yana yawo.

Sauran kasashe su yi ta kansu

“Makwabtanmu na ECOWAS na iya nemo hanyoyin da za su magance matsalolinsu yadda suka ga dama.

“Za mu iya neman tallafi daga AfDB, Bankin Duniya, EU ko kuma Asusun Kuwaiti ko kuma duk wani tushe da yake son tallafa mana wajen magance wannan matsalar.

“Amma zargin juna da barazanar yaki kamar yadda yake yi a halin yanzu ba zai haifar da komai ba sai karin bacin rai,” inji shi.