✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muhimmancin ciyarwa a watan Ramadan — Albanin Gombe

An wajabta azumi saboda muminai su kasance masu takawa.

An yi kira ga al’ummar musulmi musamman Mata da cewa su rungumi dabi’ar ciyar da marasa galihu a wannan wata na Ramadan.

Wannan kira ya fito ne daga bakin Babban Limamin Masallacin Juma’a na Miyetti da ke garin Gombe, Sheikh Adam Muhammad Albanin Gombe.

Albanin Gombe ya yi wannan fadakarwa ce a lokacin da ya gabatar da wata lakca mai taken Maraba da Ramadan, wadda Makarantar Kawthar Integrated Academy da ke unguwar Sarankiyo ta shirya.

Malamin ya yi bayani kan falalar ciyar da mai azumi yana mai cewa, “Allah Ta’ala Yana saka wa duk wanda ya ciyar da mai azumi gwargwadon ladan mai azumin ba tare da ya rage komai daga ladan mai azumin ba.”

Ya kuma ja hankalin matan da su karfafawa mazajensu guiwa wajen ba su damar ciyarwa a wannan wata mai alfarmar na azumi.

A cewarsa, azumi yana daya daga cikin rukunan Musulunci da ya wajaba a kan duk wani Musulmi baligi mai lafiya.

Ya yi bayanin cewa wajabta azumi wata hikima ce ta sanya muminai su kasance daga cikin masu takawa.

A nasa jawabin, wanda ya assasa makarantar, Malam Usman Shu’aibu, ya bayyana cewa makarantar Kawthar Integrated Academy ta shafe shekaru tana shirya irin wadannan lakcoci, don ilimantar da mata kan azumi da sauran al’amuran da suka shafi dacewa da tafarkin addinin Musulunci.

Da yake mika godiya ga shehin Malamin, ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da ilimin da suka koya, ta hanyar aiwatar da shi a aikace musamman a wannan watan na Ramadan mai albarka da kuma bayansa.

Malam Usman ya ce makarantar za ta ci gaba da hidimtawa al’umma a koda yaushe domin kyautatuwa da ci gabanta.

Wakilinmu ya ruwaito cewa matan aure da ’yan mata da dalibai da dama ne suka halarci lakcar.