✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu taimaki kanmu da kanmu

Kowane mutum  a cikinmu akwai baiwar da Allah ya yi masa, don ya amfana, kuma ya amfanar da jama’arsa. Yana da matukar alfanu mu rika…

Kowane mutum  a cikinmu akwai baiwar da Allah ya yi masa, don ya amfana, kuma ya amfanar da jama’arsa. Yana da matukar alfanu mu rika bincike don sanin irin wadannan baiwar da aka haliccemu da su, don mu san su, mu ga ta yaya za mu iya amfani da su don mu amfana kuma mu anfanar da junanmu?
Duk wanda Allah ya halicce shi mutum, to ya sani Allah ya halicce shi da wasu kafafe ko dabi’un halitta na ji da gani da tunani, don su zama ‘yanci ga dan Adam, ya amfani kansa, kuma ya amfanar da waninsa da su. Sai dai mafi yawanmu ba mu san hikimar haka ba. Za ka ga mutum cikakke, amma bai san yadda zai yi  tunanin abin da zai amfani kansa ba. Sau da yawa sai ka ga mutum cikin wahala ko kuncin rayuwa, alhalin sam bai kamata a ce yana cikin wannan halin ba.
Muna ganin kamar tunda mutum zai iya fahimtar yana son ya ji dadi, kuma yana da fahimtar bai son kunci ko wahala, kuma ya son ya samu sakewa da walwala, ai kuwa bai kamata a ce bai san hanyar tunanin yadda zai samu jin dadi da walwala a rayuwarsa ba.
To me yake sanya wasunmu daga farko har karshen rayuwarsu a wahale, alhalin wani sa’in suna da damar su canza wa rayuwarsu ko da kuwa tun daga farko haka suka tsinci kansu a takure? Mene dalilin da ya sa ba mu yin tunani kan alfanun jin dadi da walwala? Me ya sa ba mu yin tunanin daukar matakan da za su kyautata rayuwarmu, cikin ‘yanci ba?
Don me ya sa ba za mu yi duba ga tsarin rayuwar wadanda suka dace da jin dadi da walwala ba, ko mun hango tsanin da suka hau har suka kai ga gaci?
Mu sani fa Allah ma da ya halicce mu bai yarda mu bar kanmu cikin wahala da rashin ingancin rayuwa ba.
Don haka ne ma Allah ya saukake mana wasu abubuwa duk bai daya, ta yadda kowa zai iya amfana da su, ya amfani kansa ko waninsa. Misalan su kuwa a bayyana suke; su ne irin su iska da rana da ruwan sama da dai sauransu, ta yadda ba za ka je gun kowa ba don ka same su, ko ka nemi izinin yin amfani da su ba.
Kada mu manta cewar wasu mutane ba kasaifai suke fahimtar irin baiwar da Allah ya yi musu ba. Wasu kuwa sukan fahimta, amma sukan raina, saboda hankalinsu na kan wani abu da suke ganin ya fi wannan baiwar da Allah ya yi musu.
To, mu sani ba wata baiwa da Allah Ya bayar wadda ba za a yi amfani da ita wajen cimma muhimmin burin rayuwa ba. Sai dai in an raina ko ba a bincika ba.
Ba ma wannan ba, sau da yawa ma, sai ka ga wasu ga baiwar, ga damar su ji dadi ko su inganta rayuwarsu a gabansu, amma sam ba za su iya tunanin wata kirkira ba, ga wannan damar balle ma ta kai su ga jin dadin ta; misalin haka kuwa shi ne, wanda Allah ya ba shi wadatar lafiya, amma bai san ta yadda zai amfana da ita ba, balle ya san yadda zai kare kansa daga rashinta ba. A irin haka ne ma sai ka ga lafiyayye ya daura bandeji yana bara, to wannan wane dadi ya ji ga lafiyar da yake da ita, wace hanya ya bi don inganta lafiyarsa ko kareta daga salwanta? Babu.
Kuma sai ka ga mutum ya iya kere-kere da sake-sake iri-iri, amma haka kawai sai ya watsar, ya dauki hannunsa zuwa kan titi yana mika bara ko roko. Sam bai hankalta da baiwar da Allah ya yi masa don amfani da hannunsa, kila ma har ya amfanar da wasu.To ina wani jin dadi ga abin da ka samu ta hanyar bara a kan abin da hannunka ya samar maka?Babu.
Wasu kuwa basirar gane karatu da fahimtar abu cikin sauki Allah ya hore musu, amma su zauna su koya, su amfana ya gagaresu. Hasali ma sai ka tsince su suna amfani da wannan baiwar wurin koyon miyagun dabi’un da ba za su amfane su da komai ba, sai ma jaza musu muguwar wahalar rayuwa da za su yi. Idan mutum ya yi amfani da kaifin basirarsa ya koyi damfara ko zanba, ai karshensa gidan yari. To wannan wane dadin rayuwa ya samu, wane taimako ya yi wa kansa? Babu.
Wasu kuwa ga damar suna da ita, suna aiki da ita sai dai sam ba su tunanin kago hanyoyin inganta ta da kayata ta, ko canza mata fasali daga tsohon yayi zuwa sabon yayi, kullum jiya I yau, tun tana burgewa, har ta fara gundurarka, ka tsaneta. Su ma mutane su daina kulawa ko yabawa, sai ka ga ba wani ci gaba, sai dai koma baya kullum. Ka ga kuwa yin haka bai amfane ka ba. Ka rika tunani da inganta damarka ko fasahar ka, ta yadda za ka taimaka wa kanka da ita. Matsawar mutum bai jin dadin sarrafa baiwar ya kake da ita, to ba abin da yake yi illa aiki mara fa’ida; shin ko wanan hanya ce mai bullewa?Babu.
Wasu ma muhallin da suke rayuwa a cikinsa ba su san yadda za su inganta shi ba, ko don su ji dadin zama a cikinsa, musamman wadanda ke gidan haya. Don tunanin gidan ba nasu ba ne, sai ka ga mutane na ta cutar da kansu ba su ankara ba, har ta kai ga wani gidan an tara bola, babu mai kulawa a kwashe, suna ta haddasa musu sauro da kuda masu yada cututtuka ayi ta zuwa asibiti da sayen magani. Idan an tattauna hanyoyin inganta tsaftar gida, da kudin da za a kashe sam ko kusa ba za su kamo na saye magani ba.
Wai me ya sa muke ganin asarar gyaran wurin zamanmu, ba mu san duk inda kake nan ne duniyar ka ba. Idan ka ji dadin wurin, to ka ji dadin duniya; idan kuwa ba ka ji dadi ba, to ba ka ji dadin duniyar ka ba.Ko kuwa akwai mai tunanin wannan ba haka ba ne? Ni dai na ce babu.
Lallai kowane mutum ya dubi kansa ciki da waje, ya hasko baiwar da Allah ya yi masa, ya inganta ta don ya taimaka wa kansa da kansa, har ma ya taimaka wa  al’umma baki daya.
Ya Allah ka taimake mu, mu gane da baiwar da Ka yi mana, mu amfana da ita, ko mun taimaki kanmu da kammu don jin dadin rayuwarmu amin.
Ana iya tuntubar  A’isha Liman ta: 09093467171