✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Sunday Mai Sallah

A sanya masa suna Sunday Mai Sallah.

Wani mutum ne yake cikin matsalar kudi, matarsa na kwance asibiti tana nakuda.

Ya nemi taimakon masu kudi na kusa da ’yan uwa duk suka hana shi.

Aka ma rasa motar da za a kai ta asibiti, suka ce babu mai a motocinsu.

Yana cikin wannan hali sai ga wani Ibo mai tireda ya zo wucewa, ya tambaye shi abin da ke damun sa, ya gaya masa.

Nan da nan Ibon mai suna Sunday ya dauko mota, aka kai matar asibiti, ya biya kudin asibiti, ya kawo kudi ya ba shi.

Ranar da ta haihu, ya kai masa buhun shinkafa da sauran kayan jariri.

Da ranar suna ta zo, aka tambayi mai gida, wane suna za a sa wa yaron, sai ya ce: “A sanya masa suna Sunday Mai Sallah!”