✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Ni ma da kyar na cinye!

Ban ajiye maka ba ne, don na san ba za ka iya ci ba.

Wani Bafulatani ne ya kai matarsa asibiti, sai lokacin Sallar Magriba ya yi, ya tafi Sallah.

Yana can sai aka dauke wutar lantarki. Ma’aikatan jinya suka bi gado-gado suka ba su kyandir don su kunna.

Da Bafulatani ya dawo ya ga gadon kowa da haske amma na matarsa babu, sai ya je wajen likita ya ce: “Likita na ga ko’ina da haske amma ban da gadon matata.

Sai Likita ya ce an ba kowane gado kyadir ya tambayi matarsa.

Da ya dawo sai ya ce da matarsa ina abin da likita ya kawo?

Sai ta ce: “Maigida rogon birni? Ai ni ma da kyar na cinye.

“Ban ajiye maka ba ne, don na san ba za ka iya ci ba, don ni ma da kyar na cinye!”