✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Duniya mai juyawa

Baba, malaminmu na Geography ya ba mu labarin cewa, duniya haka take juyawa.

Wani yaro ne suna cin abinci da babansa, sai ya ga wata tsokar nama babba a gaban babansa, yana so ya juyo da naman gabansa.

Sai ya ce da baban: “Baba, malaminmu na Geography ya ba mu labarin cewa, duniya haka take juyawa!”

Yana fadin haka sai ya juya kwanon, yadda naman zai koma gabansa.

Sai baban ya gane wayonsa, sai ya ce: “Idan ta juya haka, sai ta kara juyawa!”

Sai ya juyo naman ya koma da shi gabansa.