✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu ne matsalar kasar nan —Rochas Okorocha

Kalilan ne daga cikin ’yan siyasa suka sa Najeriya a gabansu suke kishinta.

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha ya ce ’yan siyasar Najeriya suna taka gagarumar rawa game da rashin hadin kai a tsakanin kabilu da mabiya addini daban-daban na kasar.

Rochas wanda shi ne Sanatan shiyyar Imo ta Yamma a zauren Majalisar Dattawa, ya ce wannan matsala na barazana ga makomar ci gaba da hadin kan al’ummar kasar.

Okorocha ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka dangane da taron daurin auren Yusuf Buhari, da ga Shugaba Muhammadu Buhari da aka yi a garin Bichi na Jihar Kano a karshen makon jiya.

Ya ce yadda manyan ’yan siyasa suka hada kai a wurin auren ya nuna a fili cewa, ’yan siyasar na iya magance matsalolin kasar da kansu.

“Ai da ma mu muka kawo damuwar da ake ciki a kasar nan, ’yan siyasa ne ba kowa ba.

“Idan har muka yarda cewa ana so a samu hadin kan kasar nan ai zai yiwu,” in ji Okorocha.

Sai dai Okorocha ya bayyana dalilan da ya sa ’yan siyasa ke haifarwa da Najeriya matsaloi shi ne, yadda ake bari kowa da kowa yake shiga harkar siyasa.

“Wadanda bai kamata a ce suna siyasa ba suna siyasa, wasu siyasarsu ta kasuwanci ce ba siyasar al’umma ko ta kishin kasa ba.

“Irin wadannan su ne wanda ba su da wani buri ya wuce a samu mulki a samu kudi, daga su sai iyalansu kawai suka sani, akwai su suna nan da yawa a kasar nan.”

“Sannan akwai wadanda siyasarsu ta kabilanci ce da addini, idan ba addini ko kabilanci, su ba ruwansu, su ma suna nan da yawa a kasar nan.”

A cewar Okorocha, kalilan ne daga cikin ’yan siyasar suka sa Najeriya a gabansu suke kishinta.

Rochas ya kuma ce ya ji dadi yadda ya ga shugabannin Najeriya suka hadu a wurin daurin auren dan shugaba Buhari yana mai cewa hakan zai kawo hadin kai a Kasar.

“Najeriya ta hadu, da wadanda ma ban yi tsammanin za su halarci ba, da wadanda da ake ganin kamar ba sa shiri da shugaban kasa duk sun halarta, irin wannan taro yakan kawo hadin kai da soyayya,” a cewar Rochas.

Aminiya ta ruwaito cewa, manyan ’yan siyasar Najeriya daga jami’yyu daban-daban sun halarci daurin auren, ciki har da tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan, Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Fani-kayode, Alhaji Buba Galadima da sauransu.