✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mourinho ya zama sabon kocin AS Roma

Mourinho zai maye gurbin Paulo Fonseca a Stadio Olimpico.

AS Roma ta sanar da nada Jose Mourinho a matsayin wanda zai ja ragamar horas da ’yan wasanta a kaka mai zuwa.

Kungiyar ta bayyana hakan a wani sako da ta wallafa kan shafinta na Twitter a ranar Talata.

Sanarwar da AS Roma ta wallafa ta ce, “muna farin cikin sanar da cewa kulob din ya cimma yarjejeniya da Jose Mourinho don zama sabon kocinmu a kakar wasanni mai zuwa.”

Jose Mourinho bai bata wani lokaci mai tsawo ba sosai kafin samun aiki a wata kungiyar bayan sallamar da Tottenham ta yi masa a ranar 19 ga watan Afrilun da ya gabata.

Babu shakka dai hakar Mourinho bata cimma ruwa ba a gasar Firimiyar Ingila, inda ya kasa gamsar da kungiyoyi uku da ya yi wa aiki a baya ciki har da Chelsea, Manchester United da kuma Tottenham a baya bayan nan.

Kungiyoyin uku dai duk sun sallami Mourinho ne bayan gaza yi musu wani katabus na cimma bukatunsu.

Sai dai har yanzu ana gana kimar kocin mai shekara 58 a Italiya, inda shekaru goma da suka gabata ya yi abun a yaba a Inter Milan, kungiyar da ya jagoranta wajen lashe gasar Serie A da kuma ta Zakarun Turai a shekarar 2010.

A yanzu Mourinho zai maye gurbin Paulo Fonseca a Stadio Olimpico bayan kulla yarjejeniyar kwantaragin shekara uku da kungiyar.