✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Me ya sa ‘yan Kwankwasiyya suka so Atiku ya fadi zaben fid-da-gwani?

Ana rade-radin cewa akwai boyayyiyar yarjejeniya cewa Kwankwaso zai mara wa Wike baya

Tun bayan ficewar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, daga jami’yyar PDP, ‘yan Kwankwasiyya suke bayyana adawarsu ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Da farko ‘yan Kwankwasiyyar sun zafafa adawarsu ga Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, saboda zarginsa da suke yi da mara wa bangaren da ke jayayya da Kwankwaso a Kano a kan shugabancin jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma.

A watan Afrilun da ya gabata ne baraka ta kunno kai a reshen jam’iyyar PDP na Arewa maso Yammacin Najeriya, inda Kwankwaso ya zargi Aminu Tambuwal da yin katsalandan cikin al’amuran jam’iyyar a Jihar Kano.

Wannan zargi da Madugun Kwankwasiyyar ya yi ya tunzara magoya bayansa, inda suka dinga zafafa adawa tare da sukar kudurin Tambuwal na neman PDP ta tsayar da shi takara, a shafukan sadarwa na zamani musamman a Facebook.

Sai dai rana tsaka ‘yan Kwankwasiyyar suka sauya salon adawarsu tare kausasa hamayya zuwa kan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, tare da yin fatan rashin nasara a gare shi a zaben fid-da-gwani na jam’iyyar ta PDP.

Fitattun ‘yan Kwankwasiyya masu amfani da shafin Facebook sun yi ta yada ‘farfaganda’ da zazzafar adawa ga takarar Atiku.

A daya bangaren kuma sun nuna goyon bayansu kai-tsaye ga gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike.

Ana zargin Wike, wanda ya fito neman takarar shugabancin Najeriya a PDP, na da wata boyayyiyar yarjejeniya tsakaninsa da Kwankwaso, a kan zai ba shi daukacin daliget din da suka fito daga Jihar Kano, inda za su kada masa kuri’a a lokacin zaben fid-da-gwanin PDP.

Wasu ma har cewa suka yi wannan ne ya sa daliget-daliget din Kano suka bayyana a dandalin zaben fid-da-gwanin da huluna hana-sallah masu dauke da hoton Wike.

Sai dai da alama wannan shiri bai kai ga nasara ba domin tuni Atiku ya lashe zaben fid-da-gwanin, inda ya zama dan takarar PDP a babban zaben 2023.

Kuma ma an ambato Madugun Kwankwasiyya yana nesanta kansa da duk wani abin da ya shafi PDP ciki har da zabenta na fitar da dan takarar shugaban kasa.

Amma duk da haka ‘yan Kwankwasiyyar na ci gaba da adawa da nasarar Atiku a shafukan sadarwa da rumfunan masu shayi.

Abin tambaya a nan shi ne me ya sa ‘yan Kwankwasiyyar suka so Atiku ya fadi?

 

Buhari Abba Rano, dan jarida ne kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum daga Jihar Kano.