✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mbappe da Haaland: Shin an samu magadan Ronaldo da Messi?

Shi kansa Kaka, ba don Ronaldo da Messi da ya lashe Balon d’Or sama da daya.

A farkon kakar bana ce Kungiyar Manchester City ta dauko dan wasan gaba, Erling Haaland daga Kungiyar Dortmund ta kasar Jamus.

Yadda dan wasan ya yi kaca-kaca da Kungiyar Manchester United a makon farko da zuwansa Ingila ne ya sa magoya bayan kungiyar suke cewa lallai kakarsu ta yanke saka, domin matsalarsu ta rashin zura kwallaye ta kare.

Tun lokacin Haaland ke ci gaba da cin kasuwarsa babu kakkautawa a kungiyar, inda yake ta zura kwallaye yadda yake so.

A makon jiya ne ya zura kwallo uku rigis a ragar Kungiyar Burnley, inda kwallayensa suka kama 42 a wasa 37 da ya buga wa Kungiyar Manchester City, ciki har da kwallo biyar da ya zura a ragar Kungiyar RB Lepzig a wasan Gasar Zakarun Turai.

A kasarsa ta Norway kuwa, dan wasan ya zura kwallo 21 a wasa 23 da ya buga tun shekarar 2019 da ya fara wakiltar kasar yana dan shekara 19.

A bangaren Mbappe kuwa, dan wasan yana tashe matuka, wanda hakan ya sa kocin kasar Faransa, Didier Deschamps ya nada shi a matsayin kyaftin din kungiyar yana dan shekara 24 duk da cewa akwai manyan ’yan wasa a gabansa.

Daga cikin ’yan wasan da suke gaban dan wasan, akwai Griezman, wanda yanzu rahotanni ke nuna cewa zai bar taka wa kasar leda saboda ba Mbappe kyaftin.

Dan wasan ya zura kwallo 36 a wasa 66 da ya buga wa kasar Faransa tun shekarar 2017 da ya fara buga wa kasar ciki har da kwallo uku rigis da ya jefa a ragar tawagar Ajantina a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Duniya.

A bangaren wasannin kungiya, tun a kakar 2017 da ya je Kungiyar PSG a matsayin aro, dan wasan yake jan zarensa, inda zuwa yanzu yake da kwallo 138.

Wannan ya sa yanzu duniyar kwallo ta fara komawa kan ’yan wasan biyu.

Sai dai tambayar da ake yi ita ce shin za su iya zama magadan Ronaldo da Messi? Shin za su iya dadewa suna jan zare irin nasu?

An dade ana tafka muhawara a kan tsakanin Ronaldo da Messi wa ya fi wani, inda ake amfani da Kalmar GOAT wato Greatest Of All Time wajen bayyana wanda ya fi.

Amma ko tantama a kan su biyun suna gaba da kowa ba a yi, domin an kasa samun wanda zai dusashe tauraronsu har ma ta kai ana tunanin ba a taba samun ’yan wasa ba kamar su a tarihin tamaula.

A baya, an yi zaratan ’yan wasa, tun lokacin su Johan Cruyff da Michael Platini da su Pele da Mardona har zuwa lokacin su Zinedine Zidane da su Ronaldo na Brazil da Figo da Rivaldo da suransu.

Amma a tarihin kwallo ba a taba samun wadanda suka dade suna zamani ba kamar Ronaldo da Messi musamman a shekara goma sha zuwa 20 da suka gabata domin da wuya ka ga dan kwallo ya yi shekara 10 tauraronsa bai dusashe ba ko kuma akalla ya rage haske, amma su abin kara gaba yake yi, sai a kakar bara da aka fara ganin alamar sun fara yin kasa.

Alamar sanyinsu Ronaldo ya bar Kungiyar Manchester United ya koma Kungiyar Alnassr ta Saudiyya, inda duk da cewa yana jan zarensa a gasar kasar, ana ganin alamar sanyi domin bai kamata ya koma taka leda a wajen Turai ba.

Haka ma rahotanni sun nuna cewa sai dai ya rasa babbar kungiyar da za ta dauke shi ne ya yanke shawarar tafiya Saudiyya.

A bangaren Messi, duk da ya lashe Gasar Kofin Duniya da Ajantina, ana ganin komawarsa Kungiyar PSG ta Faransa ba ta haifar da da mai ido ba.

Kafin zuwansa kungiyar, suna lashe Gasar Ligue 1 ta kasar, inda babban burinsu shi ne lashe Gasar Zakarun Turai, amma ko a kakar bana a wasan farko na zagaye na farko ne aka yi waje da su.

’Yan wasan da Ronaldo da Messi suka hana tashe

Daga cikin wadanda tashen Ronaldo da Messi ya danne su, inda suka kasa lashe kyautar gwarzon dan wasa duk da cewa sun kware, akwai Xavi da Iniesta da Suarez da Torres da Buffon da Riberry da sauransu.

Shi kansa Kaka, ba don Ronaldo da Messi da ya lashe sama da daya.

Akwai kuma irin su Neymar da Griezman da su ma sun nuna kwarewa, amma yanzu shekarunsu sun ja ba tare da sun lashe kambin ba, har sun fara tunanin ritaya, alhalin su Messi da Ronaldo suna ci gaba da taka leda.