✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mawakiyar Duniya Tina Turner ta riga mu gidan gaskiya

Tina ta rabu da mijinta a 1978 sakamakon cin zarafi da take fuskanta daga wurinsa.

Fitacciyar mawakiya Tina Turner wacce ta shahara a duniyar waka kamar The Best da What’s Love Got To Do with It, ta rasu tana da shekaru 83 a duniya.

Tina Turner ta sha fama da matsalolin rashin lafiya da dama a cikin ’yan shekarun nan, da suka danganci ciwon daji, mutuwar barin jiki da kuma matsalar koda.

Ta yi suna tare da mijinta mai suna Ike a cikin shekarun 1960 tare a wasu wakokinta irin su Proud Mary da River Deep, Mountain High.

Tina ta rabu da mijin nata a shekarar 1978 sakamakon cin zarafi da take fuskanta daga wurin sa, inda ta ci gaba da samun nasara a duniyar mawaka a shekarun 1980.

An haife ta da sunan Anna Mae Bullock a wani kebabben asibiti na Tennessee da ke Amurka, daga baya ta auri Ike Turner ya canza mata suna zuwa Tina ta kuma dauki sunan shi na Turner, ta kasance Tina Turner.

Ta wahala sosai cikin rayuwar auren ta, inda Ike yakan yi mata duka ta yi ta fama da rauni a jiki, ta kan shiga cikin rudani don azaba, ga kuma rashin kudi a cikin shekaru 20 da tayi tana dangantaka da Ike Turner.

Sai dai ta zama tauraruwa da kanta bayan da ta cika shekaru 40, a lokacin da tauraron yawancin takwarorinta ke dushewa, kuma ta kasance babbar mai kide kide bayan shekaru har ya zuwa rasuwarta.

Mawaka masu tasowa a wancan lokaci da suka hada da Beyonce, Janet Jackson, Janelle Monae da kuma Rihanna, sun tasirantu da baiwarta.