✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mawaki 442 na nan da ransa a kurkukun Nijar’

Majiyar ta ce sabanin labarin da aka yada, 442 bai mutu ba

Bayanai daga Jamhuriyar sun tabbatar da cewa matashin mawakin nan mai suna Mubarak Abdulkarim wanda aka fi sani da Mista 442, na nan da ransa bai mutu ba.

A ‘yan kwanakin nan dai, wasu rahotanni a kafafen sada zumunta na zamani sun sha rawaito cewa mawakin, wanda aka kulle a kasar a bara saboda mallakar takardun bogi, ya mutu a kurkukun kasar.

Wani mazaunin Yamai, babban birnin kasar mai suna Ibrahim Yusuf wanda aka fi sani da Nitu Baban Pele da ke kai-kamo tsakanin hukumomin Jamhuriyar Nijar da kuma dangin Mista 442 a Najeriya, shi ya tabbatar wa Aminiya cewa mawakin na raye kuma a cikin koshin lafiya a inda yake tsare a gidan yari.

“Nakan je gidan kaso inda suke tsare, kuma zuwan da na yi a baya-bayan nan shi ne ranar Larabar da ta wuce, kuma na baro shi da abokinsa lafiya kalau” in ji Nitu Baban Pele.

Nitu ya kuma ce bisa dokar kasar, ba a shiga da waya wurinsu, amma da ya je da wayarsa ya kuma ba shi ya yi magana da wakilinmu don ya ji muryarsa.

Sannan ya ce shi da kansa ya ji jita-jitar mutuwar mawakin, ya kuma yi watsi da ita kasancewar ya san ba gaskiya ba ce.

Mista 442 shi da abokin sana’arsa Mista Ola na tsare ne gidan yarin kasar a bisa zargin mallakar takardun shaidar zama dan kasa na bogi da kuma gabatar da su don a ba su fasfo a aniyarsu ta fita kasar waje daga kasar.

Mista 442 shi ne abokin wakar jaruma Safiya Yusuf, wacce aka fi sani da Safara’u, wandanda a baya Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ta bayar umarnin kama su a bisa zargin raye-rayen batsa da kuma zargin bata tarbiyya.

Amma kafin a kama shi a Nijar, sun raba gari da jarumar a inda ta yi zargin ya yaudare ta.