✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Amurka ta yi alkawarin taimakon Najeriya

Amurka ta bayyana damuwa kan da cigaban ilimi da hadin gwiwa tsakanin kasashen.

Amurka ta kaddada kudurinta na taimaka wa Najeriya a kokarinta na magance matsalolin tsaro da ke addabarta.

Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard, ta bayyana cewa baya ga tsaro, kasarta ta kuma damu game da ci gaban ilimi da hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

“Gwamnatin Amurka ta himmatu wajen samar da mafita ga al’umma kan kalubalen tsaro da bunkasa ilimi da kiwon lafiya gami da harkar noma da kasuwanci,” inji jakadiyar.

Leonard, ta bayyana hakan ne a ranar Laraba, lokacin da Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya karbi bakuncinta a Birnin Kebbi.

Ta kuma koka game da koma baya da aka fuskanta a duniya a fannin kasuwanci da zuba jari sakamakon barkewar COVID-19 tana mai cewa gwamnatin Amurka ta kara kudade a fannin kasuwanci da zuba jarinta da zummar cike gibin da annobar ke haifarwa.

A nasa jawabin, Gwamna Bagudu ya yi kira da dorewar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannin noma da ababen more rayuwa da tattalin arzikin jiharsa.

Gwamnan ya ambaci goyon baya da jihar ta Kebbi ta samu daga gwamnatin Amurka; inda ya bukaci ganin jihar ta kara wasu fannonin hulda da Amurkar musamman a hadahadar kasuwanci.

“Muna son ganin karin hulda tare da Amurka ta fannin kasuwar zuba jari da ababen more rayuwa da aikin gona.

“Mun yi imanin hakan zai haifar da karin damar tattalin arziki da ka iya inganta alakar da ke tsakanin kasashen biyu.”