✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matthew Kukah ya sake caccakar gwamnatin Buhari

Yanayin da mutane suka tsinci kansu na da nasaba da akidarsu ta addini.

Daya daga cikin shugabannin Kiristoci a Najeriya, Matthew Hassan Kukah, ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta yi rauni musamman wajen gaza magance matsalar tsaro da ta addabi kasar nan.

Matthew Kukah ya fadi haka ne yayin wani jawabi da ya yi ta intanet ga taron wata hukuma ta Majalisar Dokokin Amurka.

A cewarsa, gwamnatin Shugaba Buhari ta gaza shawo kan matsalar tsaro da addabi kasar duk da alwashin da ta yi gabanin karbar mulki a shekarar 2015.

Ya ce sanin kowa ne cewa, shawo kan matsalar tsaro na daya daga cikin manyan alkawura da Shugaba Buhari ya yi a lokacin yakin neman zabensa na 2015.

Sai dai a yayin ganawa ta hanyar bidiyo da Hukumar Kare Hakkin Bil Adama ta Tom Lantos da ke birnin Washington na kasar Amurka, Mathew ya ce har yanzu ’yan Najeriya ba su shaida wani ci gaba da aka samu wajen magance matsalar tsaron kasar ba.

Kukah wanda shi ne shugaban darikar Katolika a Jihar Sakkwato, ya kuma zargi Shugaba Buhari da nuna kabilanci da wariyar addini wajen nade-naden mukamai a gwamnatinsa.

A cewarsa, “A yanzu ba a Arewa ba kadai, babu wani yanki a kasar da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ba su mamaye ba, wadanda suke kai hari kan al’umma a duk lokacin da suka yi ra’ayi.

“Saboda haka wannan shi ya nuna cewa akwai yiwuwar Gwamnatin Buhari ta gaza ko kuma ba ta da ra’ayin daukar wani mataki a kan lamarin.

“Babban abin da ya daure mana kai a yanzu shi ne yadda ta bayyana karara cewa Shugaba Buhari ya riki mummunar akida wajen fifita mutanen da suke kan addini daya da shi.

“Wannan shi ne karon farko a tarihin Najeriya da ya kasance dukkan bangarorin gwamnati uku Musulmi ne ke jagoranta.

“Daga kan Shugaban Kasa, Shugaban Majalisar Dattawa, Shugaban Majalisar Wakilai da kuma Shugaban Alkalai na Kasar, dukkanninsu mutanen kirki ne, amma wannan ba shi batun ba.

“A yanzu matakin adawa tsakanin Kiristoci da Musulmai ya kara tsananta, wanda hakan bai taba faruwa ba a baya.

“Labarin Leah Sharibu, (daya cikin ’Yan Matan Dapchi da har yanzu take hannun Boko Haram) ya nuna karara cewa yanayin da mutane suka tsinci kansu na da nasaba da akidarsu ta addini.

“A shekarar 2020, an kashe mana manyan limamai a Arewa, masu ra’ayin rikau suna sace mana yara sannan su tilasta musu shiga addinin Islama.

“Abin da nake son fitowa da shi a nan shi ne duk da muna ikirarin ana mulkin dimokuradiyya, amma muna da tsare-tsare da hukumomi masu rauni.

“Saboda da haka da wannan matsala da muke fama da ita, muna bukatar taimako saboda ’ya’yanmu su samu kyakkayawar makoma,” a cewarsa.

Sai dai har kawo yanzu Fadar Shugaban Kasa ba ta mayar da martani kan kalaman da Kukah ya yi ba.

A watan Afrilun da ya gabata ne mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya mayar wa da Mathew Kukah martani kan wasu kalamai da ya yi a ranar bikin Ista.

A wancan lokaci, Kukah ya ce ta’addancin mayakan Boko Haram ya kara ta’azzara a zamanin mulkin Shugaba Buhari.

Da yake mayar da martani, Garba Shehu ya ce Mathew Kukah yana cusa siyasa a sha’anin addini wanda a cewarsa kalaman da ya yi ba furuci ne ya kamata ya fito daga bakin malamin addini ba.

“Furucin da Kukah ya yi na cewa ta’addancin Boko Haram a yanzu ya munana fiye da kafin zuwan Gwamnatin Buhari a shekarar 2015, ba magana ba ce da ta kamata a ce ta fito daga bakin mai ikirarin shi malamin addini ne.

“Saboda haka Kukah ya je Borno ko Adamawa ya tambayi mazaunansu ko akwai bambanci da aka samu tsakanin shekarar 2014 da shekarar 2021,” a cewar Malam Garba.