✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin da ya haura gidan makwabciyarsa ya gurfana gaban Kuliya

A ranar Alhamis ne wani matashi mai shekaru 33 a duniya, ya gurfana a gaban wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Unguwar Rigasa a Jihar…

A ranar Alhamis ne wani matashi mai shekaru 33 a duniya, ya gurfana a gaban wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Unguwar Rigasa a Jihar Kaduna kan zargin sa da ketare iyakar gidan wata makwabciyarsa inda ya satar mata kaya da kimarsu ta kai N827,000.

Insfeta Sambo Maigari, Jami’in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotun ya bayyana cewa, mutumin ya aikata laifin ne tare da wasu biyu a ranar 20 ga watan Dasimbar bara a yankin Bakin Ruwa a Jihar ta Kaduna.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa matashin ya haura gidan ne bayan matar ta yi tafiya Abuja ya kuma satar mata dukiya.

Insfeta Maigari ya ce matashin da abokanan da suka aikata wannan ta’asa, sun yashe kayan jere na dakin girki da Labule, da jannareta da kayan abinci da takardar shaidar karatu da kudade masu tari yawa.

Jami’in dan sandan ya bukaci kotun da ta bayar da belin wanda ake zargin ta yadda zai taimaka musu wurin zakulo ragowar mutanen da ake zargin suna da hannu a cikin wannan aika-aika.

Alkalin Kotun Mai Shari’a, Malam Salisu Abubakar-Tureta, ya ba wanda ake zargi beli amma da sharadin bayar da mutumin da zai tsaya masa sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 2, ga watan Fabrairun 2021 domin ci gaba da sauraron karar.