✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashin da ake zargi da tattaka Kur’ani ya sha da kyar a Kano

Saura kiris fusatattun matasa su kawar da shi daga doron kasa.

Wani matashi da ake zargi da yagawa da kuma tattaka Kur’ani a Jihar Kano ya sha da kyar bayan jami’an Hukumar Hisbah sun ceto shi daga hannun fusatattun matasan da saura kiris su gama da shi.

Majiyar Aminiya ta tabbatar da cewa, jami’an Hukumar Hisbah ne suka ceci matashin mai shekara 20 daga hannun fusatattun matasan da suka zarge shi da wulakanta littafin mai tsarki a Unguwar Kuntau da ke Karamar Hukumar Gwale a birnin Dabo.

Matashin wanda ba a kai ga tantance sunansa ba da ke sana’ar gadi ya shiga hannun rundunar ’yan sanda Jihar Kano bayan ceto shi da jami’an na Hisbah suka yi kamar yadda mai magana da yawun rundunar ’yan sandan na Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar.

Kiyawa ya ce a halin yanzu suna tsare da matashin wanda tuni bincike ya kankama a kan afkuwar lamarin.

Kazalika, wani dan uwan mai gidan da matashin yake aikin gadi, Sunusi Ashiru, ya shaida wa Aminiya cewa matashin da kyar ya sha domin kuwa bayan dawowarsa ya riski fusatattun matasa rike da makamai iri-iri da suka yi kokarin kawar da shi daga doron kasa.