✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi Ya Kashe Yaro Ya Jefa Gawar A Kan Soro

Ana zargin ya aikata laifin ne a unguwar Bachirawa da ke Kano a farkon makon nan.

Ana zargin wani matashi mai shekara 21 da kisan wani yaro mai shekara uku sannan ya jefa shi a kan dakin gidansu.

Ana zargin ya aikata laifin ne a unguwar Bachirawa da ke Kano a farkon makon nan.

Mahaifin yaron, Malam Nura Lawan ne ya bayyana wa ’yan jarida a fadar Sarkin Kano, bayan dagacinsu ya je wa da Sarkin rahoton abin da ya faru a unguwar tasa, a zaman fada na ranar Laraba.

Mahaifin yaron ya bayyana cewa wanda ake zargi, ya kira dansa Aliyu Nura mai shekara uku gidansu, ya kulle kofa, ya halaka shi ba tare da kowa ya sani ba.

“Da babar wanda a ke zargi ta dawo ne, sai kannensa suka fada mata cewa sun ga wanda ake zargi ya jefa wani abu a kan soro, ita kuma ba ta ce komai ba.” In ji Malam Nura.

“Sai da babansu ya dawo ta fada masa cewa dan nasu ya jefa mata kayan wanki a saman daki”.

“Shi kuma maigida ya hau sama don ya gani, da hawan sa, sai ya ga gawar yaro, kurma ya ihu.”

Malam Nura, ya kuma ce, “Ni na fara zuwa wurin da na ji ihunsa, sai na ga ashe dana ne da ake ta nema”.

Sannan ya kara da cewa, tuni ’yan sandan Bachirawa sun kama wanda ake zargi an kuma kai maganar shelkwatar ’yan sanda ta jihar don ci gaba da bincike.

A jawabinsa dangane da abin da ya faru, Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ta bakin Wazirin Kano Sa’ad  Shehu Gidado, ya umarci masu unguwanni da su rika kai rahoton bata-gari a cikin al’umma, ba sai sun aikata laifi ba tukunna.