✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar Sanata Bello Hayatu Gwarzo ta rasu

Allah Ya yi wa matar Sanata Bello Hayatu Gwarzo, Hajiya Hauwa rasuwa. Sanata Bello Hayatu Gwarzo, tsohon sanata ne mai wakiltar Kano ta Arewa a…

Allah Ya yi wa matar Sanata Bello Hayatu Gwarzo, Hajiya Hauwa rasuwa.

Sanata Bello Hayatu Gwarzo, tsohon sanata ne mai wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattijai na tsawon shekara 12, kafin Sanata Barau Jibril ya maye gurbinsa.

A ranar Alhamis 22 Oktoba 2020 Allah Ya yi wa mai dakin nasa rasuwa, kuma tuni aka yi jana’izarta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da sauran jami’an gwamnati da ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban ne suka halarci sallar janazar.