✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mataimakiyar Shugaban Ajentina ta sha da kyar daga yunkurin harbe ta

Maharin ya zaro bindiga zai harbi Cristina a kofar gidanta

Matimakiyar shugabar kasar Ajentina Cristina Kirchner ta tsallake rijiya da baya yayin da wani mutum dauke da bindiga ya yi kokarin harbe ta a cikin taro.

Shugaban kasar ya ce, Mutumin ya kai wa Cristina Kirchner harin ne a kusa da gidanta a birnin Buenos Aires a ranar Alhamis.

Mutumin wanda ba a san ko wane ne ba, ya tunkari Cristina ne yayin da ta fito daga mota, mutane kuma suka kewaye ta, shi kuma ya shiga cikinsu cewa za ta sa masa hannu a takardar nuna kauna gare ta.

Amma da ya matso kusa, sai ya fito da bindiga ya kuma aunata cikin shirin harbi, amma bindigar ta ki tashi, ita kuma ta kauce.

Kafofin yada labaran kasar sun nuna bidiyon mutumin a lokacin da ya fito da bindiga, ya kuma auna mataimakiyar shugaban kasar a kusa-kusa da niyyar harbe ta, ita kuma ta sunkuyar da kanta ta shige mota.

Ministan tsaro na kasar, Anibal Fernendez, ya ce, an kama mutumin, kuma ’yan sanda na gudanar da bicike kan faruwar lamarin.