✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu ruwa-da-tsaki sun auna ayyukan Hukumar NSC

Masu ruwa-da-tsaki a harkar sufurin jiragen ruwa sun tabbatar da cewa nada Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), da aka yi a…

Masu ruwa-da-tsaki a harkar sufurin jiragen ruwa sun tabbatar da cewa nada Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), da aka yi a matsayin mai daidaita al’amura a harkar tatttalin arziki ya kawo canji mai amfani a banagen.

Shugaban kungiyar Masu Jiragen Ruwa ta Najeriya (NISA), Malam Aminu Umar, ya ce an samu sauye-sauye masu ma’ana tun lokacin da Gwamnatin Tarayya ta nada Hukumar NSC a matsayin mai daidaita harkokin hada-hadar tashar jiragen ruwa kimanin shekara biyu da suka gabata.

Malam Umar ya ce Hukumar NSC ta shiga tattaunawa da masu ruwa-da-tsaki a wannan masana’anta, inda ya ce mafi yawan masu ruwa-da-tsaki sun rika tatttauna yadda za a rage kudin harajin jiragen fiton kaya a tashoshin jiragen da kuma harajin dadewa a tashoshin ka haifar musu.

Ya ce, “A wannan fanni, ina ganin Hukumar NSC tana gudanar da ayyuka da dama. Wani babban aikin da suke yi, shi ne shirye-shiryen wayar da kai, inda suke ilimantar da dimbin masu hada-hadar sufurin jiragen ruwa kan hanyar da ta dace da yadda za su ribaci wani alfanu ko da an samu rikici a tsakanin bangarorin da suke harkar. Don haka ina ganin suna yin aikin da ya kamata a wannan sabon matsayi da aka ba su.”

Shi kuwa Shugaban kungiyar Masu Dakon Kaya da Gwamnati ta Amince da su (NAGAFF), Dokta Eugene Nweke, ya yi nuni da cewa abin da NSC ta yi a shekarar da ta gabata, shi ne kawar da duk wata katanga ta hanyar gano masu gudanar da ayyukansu a wannan fanni da suke bukatar kula.

Nweke ya ce Babban Sakataren Hukumar NSC, Hassan Bello ya kawo yadda za a shawo kan dimbin matsalolin da ake fuskanta ta hanyar samar da daidaitaccen farashi, al’amarin da ya ce an shi cikin shekara guda.

Ya ce, “Kuma sun tabbatar da tsarin wayar da kai ta hanyar fadakarwa, wadda a yau, babu wanda zai ce ba ya da masaniya game da Hukumar NSC da sabon matsayinta. Ina ganin sun tabo manyan sassa na wannan. A wannan tsakani, Hukumar NSC ta kai ga Majalisar Zartarwa ta kasa da Majalisar Dokoki ta kasa don tabbatar da ayyukanta a karkashin doka. Wannan na nufin duk wani mai tababa da ke ikiarin cewa ba su da ikon daidaitawa da gudanar da al’amura bisa sahalewar doka, lallai ya san cewa yana tafka kuskure.

“Sannan, Hukumar NSC ta nuna cewa wasu ayyuka da ake gudanarwa a wannan masana’anta da suke kawo tarnaki ga ci gaban hada-hadar tashar jiragen ruwa da na kasuwanci a fadin duniya, dole a kawar da su, amma sai aka kai karar ta kotu, ba ma karamar kotu ba, har ma zuwa Babbar Kotu, inda aka biyo baya da Kotun daukaka kara. Akwai dimbin abubuwan da muke son ganin Hukumar NSC ta aiwatar da su, ta hanyar kyale kotu ta warware wadannan matsaloli don su zama izina ga masu hada-hada. Kuma suna kan turbar daidai.

“Yanzu, ta amfani da dimbin korafe-korafen da ta karba bayan da ta zamo mai daidaita al’amura, akwai dimbin korafe-korafe da wasiku a gabansu, kuma suna ba su kula gwargwadon dacewarsu. Idan aka samu mutumin da ya mallaki jirgin ruwa ko jirage biyu, wadanda hukumar ta kawo musu dauki za a samu gamsuwa kan yadda hukumar ke gudanar da ayyukanta. Ta yaya ake tantance kimar aikin sashen sauraren korafi? Ana daukar mataki a kan lokaci. Kuma babu wani korafi da ya isa wannan sashen ba tare da an ba shi kulawa a wannan rana ba.”

Game da tabbatar da ana aiki da ka’ida Nweke ya ce bai kamata wani ya manta cewa wannan sashe na sufurin jirage cike yake da masu hana ruwa gudu ba, wadanda ya yi zargin cewa suna yunkurin dakile Hukumar NSC daga aiwatar da ayyukanta ta hanyoyi da dama, “ciki har da bayar da cin hanci idan zai yiwu.” inji shi. Ya kara da cewa amma hukumar tana nan a kan bakanta.

“Don haka daga yadda ake a yanzu, NSC a tsawon shekara biyu ta nuna a shirye take ta yi aiki. Kuma ina fata kuna sane da dimbin albarkatun da ake kashewa wajen horar da ma’aikata a Hukumar NSC don sake fasalin ma’aikatan su fuskanci kalubalen da ke gaba. Kuma duk wata hukuma da take son samun nasara irin wannan, kodai tana cikin harkar tashoshin jiragen ruwa ne ko ta fahimci harkar jiragen ruwa. Wannan shi ne abin kawai zai kai su ga gaci,” inji shi.

Game da yadda Hukumar NSC take samun hadin kai bisa tsarin yadda gudanarwarta zai kasance, ya ce akwai abubuwan da ke haddasa tarnaki, wannan kuma shi ne asalin abin da yake faruwa. “Ba za a ce ya mutu murusba, amma dai tuni ginin ya riga ya fadi saboda matakin da rashawa ke takawa a tsakanin masu gudanarwar. Idan har ka gamsu da haka, to za ka fahimci cewa akwai wasu abubuwa da aka yi na hobbasa bisa tsarin doka da kuma yarjejeniyar fahimta, wadda gwamnati ta sanya hannu ta hanyar hukumominta.

A wannan gabar, dole ne Hukumar NSC ta mai da hankali wajen neman shawarwari da tarurrukan tattaunawa da za su taimaka mata gaya. Don haka muna fatan su yi hakan bisa kwarewarsu, a cikin watanni shida masu zuwa, muna fatan ganin kwakkwaran canji. Wadannan tsalle-tsalle su zo karshe. Amma babban abin da ya kamata a fahimta a nan shi ne, karbar kudi kan aikin da ba a yi ba, an kauce masa, domin yanzu Hukumar NSC tana aiki.

“Game da dokokin, dole ne mu tuna cewa wannan fa galibi ta ginu a kan doka ne saboda batutuwa ne da suka shafi doka. Don haka wajibi ne a yi amfanin da wannan damar wajen hukunta wadanda aka kama da laifi. Akwai bukatar a samu haka daga gwamnati sannan a rattaba takarda a kansa. Amma dole ne a fuskanci batutuwan daya bayan daya don kauce wa tauna taura biyu a baki lokaci guda,” in ji shi.

Galibin bayanan masu ruwa-da-tsaki suka yi kan Hukumar NSC a matsayinta ta mai tsara tattalin arziki a shekara daya da rabi, sun nuna irin nagartaccen karbuwar da shirin ya yi, sannan a lokaci guda yake nuni da irin nasarar da za a iya samu a nan gaba.

Kawo yanzu masu ruwa-da-tsaki da wani bangare na ’yan jarida sun tabbatar da cewa Hukumar NSC tana aiki tukuru, amma dai tana matukar bukatar sake fasali don sarrafa al’amuranta yadda ya kamata. Sannan suka kara da cewa bai kamata NSC ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin hadin gwiwa da kamfanonin da ba na gwamnati ba, sannan da fadada ayyukan wajen da suka dace don samun nagarta mai dorewa.