Mutanen da suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya ya kai 15,181 bayan karin mutum 627 sun kamu da cutar a jihohi 23.
Haka kuma yawan wadanda suka warke daga cutar a Najeriya ya karu zuwa 4,891 a jihohi 35 da kuma Abuja.
Alkaluman Hukumar Yaki da Cutttuka Masu Yaduwa (NCDC) na ranar Juma’a 12 ga watan Yuni sun nuna mutum 9,891 ne suka rage dauke da cutar a Najeriya.
Ta kara da cewa zuwa ranar an yi wa mutum 88,432 gwajin cutar wadda ta yi ajalin mutum 399 a kasar.
- Mutum 92 sun warke daga COVID-19 a rana guda a Legas
- Coronavirus: An kwaso ‘yan Najeriya 102 daga Masar
Jihohin da aka fi samun bullar cutar a ranar su ne Lagos-229, Abuja-65, Abia-54, Borno-42 da kuma Oyo-35.
Jihohin mafiya wayawan masu cutar coronavirus a Najeriya su ne Legas-6,840 da Abuja-1,162 sai kuma Kano-1,049.