✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masallacin Kudus: Majalisar Tsaro ta MDD ta kira taron gaggawa

Ziyarar Ministan Tsaron Cikin Gidan Isra'ila, Ben Gvir, Masallacin Kudus ta janyo fargaba da kuma tofin Allah tsine

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taron gaggawa a ranar Alhamis, kai tayar da jijiyoyin wuya da ya biyo bayan ziyarar da Ministan Isra’ila ya kai Masallacin Kudus.

Ziyarar da Ministan Tsaron Cikin Gidan Isra’ila, Ben Gvir, ya kai Masallacin Kudus a ranar Talata ta janyo fargaba da kuma tofin Allah tsine daga sassan duniya.

Wakilin Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, ya ce, “Taron zai tattauna ne musamman kan keta haddin Masallacin Kudus da Ben Gvir ya aikata.”

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron ne bayan bukatar hakan da kasashen China da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Al’ummomi da hukumomi a sassan duniya sun bayyana shigar Masallacin Kudus da Ben Gvir, wanda hannun daman Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ne, a matsain neman tayar da zaune tsaye.

A baya dai, an sha samun dauki-ba-dai tsakanin Yahudawa da Falasdinawa, a wurare masu alfarma a birnin Kudus.

Tun da farko, kungiyoyin Faladisnawa a Yankin Gaza sun ce, “Zuwan Ben Gvir Masallacin Kudus na da matukar hadarin da zai tunzura Faladinawa.”

Ben Gvir shi ne shugaban jam’iyyar Yahudawa ta Otzma Yehudit da ke samun goyon bayan al’ummar Yahudawa masu tsattsauran ra’yi.

Samun goyon bayansa ya taimaka wa Netanyahu wajen samun nasara a zaben watan Nuwamba, bayan ta yi adawa da shi na tsawon wata 18.

A ziyarar da ya kai ranar Talata, Ben Gvir, ya ce, “Masallacin Kudus shi ne wuri mafi muhimmanci ga Yahudawa a doron kasa, kuma Musulmi da Kiristoci na ziyartar sa.”

Kulla alakar Netanyahu da ’yan adawa masu fafutukar kare hakkokin al’ummomi marasa rinjaye ya haifar da fargaba da kuma zargi daga gwamnatin Amurka.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana goyon bayanta wajen kare tarihi, “kuma ba za mu goyi bayan duk wani yunkuri na kawo rikici ba.”