✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan wasannin da za a fafata a Gasar EPL da Laliga

Manchester City za ta barje gumi da Manchester United, Real Madrid da Sociedad.

Kamar kowane karshen mako, wannan makon ma akwai wasanni a gasar Firimiyar Ingila masu daukar hankali da za a fafata tsakanin kungiyoyi.

Ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Liverpool za ta karbi bakuncin West Ham United a filin wasa na Andfield da misalin karfe 6:30 agogon Najeriya.

Wasa ne da zai dauki hankalin masu kallo duba da irin kokarin da kowace kungiya ke yi a gasar.

A haduwar farko da aka yi a watan Nuwambar 2021 a tsakanin kungiyoyin biyu, West Ham ta yi nasara a kan Liverpool da ci 3-2.

Liverpool na mataki na biyu da maki 60, yayin da West Ham ke na biyar da maki 45 a gasar.

A ranar Lahadi kuwa, wasa mafi daukar hankali shi ne karawa da za a yi tsakanin kungiyoyin hamayya biyu, wato Manchester City da Manchester United.

Za a take wasan da misalin karfe 5:30 agogon Najeriya, a filin wasa na Etihad.

Manchester City za ta karbi bakuncin Manchester United, don gwada kwanjin juna.

Manchester City ce ke samun teburin gasar da maki 66, yayin da Manchester United ke mataki na hudu da maki 47.

A haduwar farko da kungiyoyin suka yi, Manchester City ce ta yi nasara a kan Manchester United da ci 2 har gida.

Kungiyoyin biyu sun hadu sau 184 a gasar Firimiyar Ingila, Manchester United ta yi nasara sau 76, Manchester City kuma ta yi sanara sau 55, sai kunnen doki da suka yi sau 53.

Fafatawar Gasar Laliga

A gasar Laliga ta kasar Spain kuwa, Real Madrid ce za ta karbi bakuncin Real Sociedad, a filin wasa na Santiago Bernabeu da misalin karfe 9 na dare agogon Najeriya.

Real Madrid ce ke kan gaba a teburin gasar da maki 60, yayin da Sociedad ke mataki na shida da maki 44.

A haduwar farko a gasar Madrid ta doke Sociedad da ci 2 har gida.

Madrid da Sociedad sun hadu sau 173, Real Madrid ta yi nasara sau 96, Real Sociedad ta yi nasara sau 36, sai kunnen doki sau 41 da suka yi.

A ranar Lahadi kuwa a gasar ta Laliga, wasa mafi daukar hankali shi ne wasan da Real Betis za ta karbi bakuncin Atletico Madrid.

Za a take wasan da misalin karfe 9 na agogon Najeriya, a filin wasa na Benito Villamarin da ke birnin Sevilla.

A haduwar farko a tsakanin kungiyoyin da suka yi, Atletico Madrid ta doke Real Betis da ci 3 ba ko daya.

Kungiyoyin biyu sun hadu sau 131 a gasar Laliga, Atletico Madrid na da nasara sau 69, yayin da Betis ke da nasara sau 32, sai kunnen doki da suka yi sau 30.