✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Manchester United za ta dauki Ralf Rangnick a matsayin sabon koci

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta dauki Ralf Rangnick a matsayin sabon mai horas da ’yan wasanta. Hakan dai na zuwa ne bayan…

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta dauki Ralf Rangnick a matsayin sabon mai horas da ’yan wasanta.

Hakan dai na zuwa ne bayan kungiyar da ke buga gasar Firimiyar Ingila ta sallami kocinta, Ole Gunnar Solskjaer a makon da ta gabata.

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, fitaccen dan jarida a kan sha’anin kwallon kafa, Fabrizio Romanio, ya ce tattaunawa ta yi nisa tsakanin United da Ralf Rangnick don ganin an cimma matsaya.

Kazalika, kafofin watsa labarai na Turai sun ruwaito cewa sabon kocin zai jagoranci horas da ’yan wasan a Old Trafford zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Masu ruwa da tsaki a harkar tamaula sun ce tsohon kocin na kungiyar RB Leipzig uban gida ne ga manyan koca-kocan kungiyoyin Chelsea, Thomas Tuchel, Bayern Munich da ke hannun Julian Naggelsmann da kuma Jurgen Klopp na Liverpool.

Sai dai kawo yanzu babu wani tabbaci a hukumance da kungiyar ta Manchester United ta fitar kan daukar kocin.

A nasa bangaren, Ralf Rangnick yana so yarjejeniyar da United za ta kulla da shi ta zamana cewa ko da ya ajiye aikin horas da ’yan wasa a kungiyar, yana so kuma ya kasance cikin majalisar wadanda za a rika tuntuba da kuma bayar da shawara gabanin kungiyar ta zartar da wani hukunci.