✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mamman Daura na cikin koshin lafiya’

Dan Mamman Daura ya ce mahaifinsa na nan lafiya kalau sabanin jita-jitar da ake yadawa

Wani da ga dan wan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Mamman Daura ya ce mahaifinsa na nan lafiya kalau sabanin rahotannin kafafen yada labarai cewa ba shi da lafiya.

Muhammad Mamman Daura ya tabbatar da cewa mahaifinsa ba ya fama da matsalar cutar mafitsara ko ta numfashi kamar yadda ake jita-jita.

Ya ce, “A ‘yan kwanakin nan, tilas ta sa muna ta karyata wasu kirkirarrun labarai da ke cewa mahaifinmu ba shi da lafiya; wannan labarin kanzon kurege ne. Alhamdulillah baba yana nan kalau.

“Ga wadanda ke yada labarin har ma suke jin dadi ya kamata su san cewa babu wanda zai dawwama.

“Masu turo mana da sakon fatan alheri da addu’o’i kuma muna godiya”, inji Muhammad.

Wani sabon bidiyon da ke nuna Malam Mamman Daura dai ya bayyana, ko da yake Aminiya ba ta kai ga tantance lokacin da aka dauke shi ba.

Idan za a iya tunawa, a kwanan nan ne dai Mamman Daura ya fita waje domin ganin likitan da ya saba yi lokaci zuwa lokaci wanda cutar COVID-19 ta kawo wa tsaiko.

Rahotanni sun nuna cewa Mamman ya bar Najeriya zuwa birnin London na kasar Birtaniya ne a ranar Laraba.

Wata majiya da ke da kusanci da shi ta tabbatar da cewa an jima da tsara tafiyar kamar yadda ya saba yi kafin daga bisani annobar COVID-19 ta kawo tsaiko.