✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mali ta kori Jakadan Faransa daga kasarta

Jamus ta soki matakin da gwamnatin mulkin sojan Mali ta dauka.

Majalisar mulkin soji a Mali ta kori jakadan kasar Faransa daga kasarta, matakin da ke dasa ayar tambaya kan tawagar dakarun sojin Faransa da ke yaki da ’yan ta’adda a Malin.

Gwamnatin Mali dai ta ce ta bai wa jakadan Joel Meyer kwanaki uku kacal da ya bar kasar wanda tuni ma kasar Faransa ta yi wa jakadan nata kiranye.

Rikicin tsakanin Mali da Faransa na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da gwamnatin Mali ta bayar da umurnin ga sojojin Denmark da ke cikin rundunar sojin Faransa na Takuba da su bar kasar.

Dangantaka dai ta kara tsami tsakanin Mali da kawayenta na Turai tun bayan da shugaban rikon kwarya na mulkin Soji a kasar kanal Assimi Goita ya sanar da jinkirta gudanar da zaben da zai mayar da kasar tafarkin dimokradiya zuwa shekarar 2026.

‘Muna nazari kan kasancewar sojojinmu a Mali’

Faransa ta bayyana cewa nan da tsakiyar watan Fabrairu za ta yanke shawara tare da kawayen ta na kungiyar EU game da matsayin sojojinta a Mali, kwana guda bayan da gwamnatin mulkin sojin kasar ta umarci jakadan Faransa da ya fice daga kasar.

An yanke hukuncin korar jakadan ne saboda kalaman “kiyayya” da ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian da wasu jami’ai suka yi, wanda ya haifar da shakku kan goyon bayan da sojojin Faransa ke ba kasar Mali, wadda kasar Faransa ta yi wa mulkin mallaka, kuma kawar Mali da ke yaki da ‘yan tada kayar baya.

Kakakin gwamnatin kasar Gabriel Attal ya shaida wa gidan rediyon Franceinfo cewa a bayyane yake cewa lamarin ba zai iya ci gaba da tafiya haka ba.

Attal Ya ce Paris da takwarorinta na Turai da ke cikin tawagar musamman ta Takuba za su yi aiki daga yanzu zuwa tsakiyar watan Fabrairu don yanke shawara kan duk wani sauye-sauyen da za a yi na tura sojoji zuwa Mali.

Jamus ta soki matakin

Sai dai kuma a wannan Talata Jamus ta soki matakin da gwamnatin mulkin sojan Mali ta dauka na korar jakadan Faransa a matsayin “mara gaskiya” tare da cewa ta tsaya kai da fata da kawayenta na Faransa.

Korar jakadan Faransa ba tare da kwakkwarar hujja ba ya munana, a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Jamus a shafinta na Twitter.

Kasar Jamus dai na da sojoji kusan 1,500 a kasar Mali a matsayin wani bangare na tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA da kuma tawagar EU na horar da sojojin Mali.