Wani malami a Jami’ar Prince Abubakar Audu, Ayingba da ke Jihar Kogi ya mutu jim kaɗan bayan da ya yi lalata da ɗalibarsa a ɗakin otel.
’Yan sanda sun tabbatar da mutuwar malamin mai suna Mista Olajide Abimbola Ibikinle, bayan ya kammala saduwa da ɗalibar sashen da yake koyarwa ɗakin otel ɗin.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Kogi, William Aya, ya bayyana cewa ɗalibar mai suna Glory Ojochegbe Samuel, ce ta sanar da ma’aikatan otel ɗin bayan da ta lura malamin ya daina motsi jim kaɗan bayan sun kammala saduwa.
Daga nan suka garzaya da shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar cewa rai ya riga ya yi halinsa.
- Tinubu ya naɗa ɗan IBB shugaban bankin manoma
- Dalilin da ya sa aka sauya sunan Jami’ar Maiduguri — Ma’aikatar Ilimi
Aya ya bayyana cewa tuni aka tsare ɗalibar a ofishin ’yan sanda na yankin Ayingba, inda daga nan aka wuce da ita zuwa hedikwatar ’yan sanda da ke Lokoja, babban birnin jihar.
Ya ci gaba da cewa rundunar tana bincikar ɗalibar kuma da zarar an kammala za a ɗauki matakin da ya dace.
Hukumar gudanarwar Jami’ar Prince Abubakar Audu, ta tabbatar da faruwar lamarin wanda ta bayyana a matsayin abin takaici da ya ɗauki hankalin jama’a.
A saƙon ta’aziyyar da jami’ar ta fitar, ta jajanta wa iyalan Mista Olabode, ta tabbatar da cewa ’yan sanda na bincike a kan mutuwar malamin na Ilimin Kimiyyar Halayyar Ɗan Adam.
Sanarwar da Rajistaran Jami’ar, Barista Yahaya Segun Aliu, ya fitar ta bayyana takaici bisa yanayin da ya mutu a yayin da yake tarayya da ɗalibarsa.