✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makomar Shugaban PDP na tangal-tangal kan zabin mataimakin Atiku

Gwamnoni 11 sun kaurace wa taron jam'iyya; Ortom ya caccaki Atiku; Fayose ya soki takararsa

Makomar Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Dokta Iyorchia Ayu, na tangal-tangal bayan wasu da manyan shugabannin jam’iyyar sun ci gaba da guna-guni kan zabin Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar.

Wasu masu guna-gunin na kira da a tisa keyar Ayu, wasu kuma na sukar tsayar da Atiku Abubakar daga  yankin Arewa a matsayin dan takarar shugaban kasa, waku kuma za zargin shi da yin gaban kansa.

Aminiya ta samu bayanai cewa masu hankoron darewa kan kujerar shugaban jam’iyyar ta PDP sune kanwa uwar gami wajen yayata cewa an kori Ayu daga mukamin.

Amma hadimin Ayu na musamman,  Simon Imobo-Tswam, ya ce labarin da ke yawo cewa an maye gurbin uban gidansa da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Shiyyar Arewa, Ambasada Umar Damagum, a matsayin riko, “soki-burutsu ne’’.

Ya ce: “Hutun mako biyu Dokta Ayu ya dauka daga ranar 21 ga watan Yuni, 2022; Mako mai zuwa zai dawo, ranar 6 ga watan Yuli, 2022, ya ci gaba da aiki.

“Don jama’a su yi watsi da wannan shirmen da ke yawo a kafofin sada zumunta, makirci ne irin na marasa abin yi.”

Gwamnonin PDP sun kaurace wa wa taronta

Duk da haka alamu sun kara bayyana rabuwar kawuna a uwar Jam’iyyar PDP inda aka ga gwamnoninta 11 daga cikin 13 sun kaurace wa taron da Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa ya kira a ranar Laraba domin rantsar da kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar gabanin zaben Gwamnan Jihar Osun da ke tafe.

Duk da cewa gwamnonin jam’iyyar guda 10 ne ke cikin kwamitin mai mutum 128,  gwamnonin biyu kacal ne suka halarci taron — Okowa da kuma Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku.

A jawabinsa a wurin taron, Mukaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Umar Damagum, ya ce babban aikin kwamitin shi ne kai jami’yyar ga nasara a zaben na gwamnan na Osun saboda muhimmancinsa ga zaben shugaban kasa na 2023.

“Na tabbata da irin mutanen da ke cikin wannan kwamiti, Jihar Osun ta riga ta zama tamu; amma duk da haka babban aikin da ke gabanku shi ne hada kan masu ruwa da tsaki na jam’iyya a jihar”

Shi ma a jawabinsa, Okowa ya yi kira ma masu ruwa da tsaki na PDP a Jihar Osun da su hada kai wajen tabbatar da kayar da gwamnatin APC a jihar.

A cewarsa, “Kan APC ya riga ya rabe a jihar, amma duk da haka kada mu yi sanya.”

Wike muka zaba wa Atiku —Ortom

Barakar ta PDP kan zabin dan takarar mataimakin shugaban kasa ta kara fitowa fili bayan Gwamnan Jihar Binuwai, Samuel Ortom, mamba a kwamitin neman dan takarar mataimaki da dan takarar  shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar, ya kafa ya ce ba Okowa suka zaba mishi ba.

Ortom ya shaida wa tashar talabijin ta Arise TV cewa, daga cikin mutum 17 da ke kwamitin, “14 sun amince cewa Nyesom Wike za a dauka, amma abin takaici sai Atiku ya dauki Okowa a irin tasa hikimar.”

Ya ce, “Ba yadda za a yi ka yi watsi da shawarar kwamitin da kai da kanka kafa, kuma abin ya yi wa mutane dadi.”

Otrom ya bayyana cewa, “Tunda Atiku ya san ba zai dauki shawarar kwamitin ba, da tun da farko sai ya kira Wike ya sanar da shi, amma ba yi ba; Babu yadda za a yi ka rika yin abin da ka ga dama kuma ka ce mutane za su ji dadi.” 

A cewarsa, kamata ya yi “Atiku ya je ya sami Wike su tattauna a samu mafita tunda Wike babban gimshiki ne a jam’iyyar.

“Yanzu haka babu wanda ya fi Wike bayar da gudunmmawa wajen kawo wa jam’iyyar PDP cigaba.”

Ortom wanda ya ce yanzu ya shiga tunani da addu’o’i, ya zargi Atiku da rashin yin abin da ya kamata wajen hade kan jam’iyyar. 

Da aka tambaye shi game da ko zai mara wa Atiku Baya, sai ya ce, “Idan na gama addu’o’ina, duk abin da Allah Ya umarce ni, shi zan yi.” 

A ba Kudu shugaban kasa ko a hakura —Fayose

A daya bangaren kuma, tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya tayar da kura inda ya dage cewa dole dan takarar shugaban kasa da PDP ta tsayar a zaben 2023 ya zama daga yankin Kudu.

Fayose ya bayyana cewa abin kundin tsarin mulkin jam’iyyar PDP ya tanadi karba-karbar mulki domin tabbatar da adalci ga kowane yankin siyasa, don haka yanzu lokaci ne da yankin Kudu za su mulki Najeriya.

“Shugabancin Najeriya na yanzu yankin Arewa ne suka yi, kuma wa’adi biyu, saboda haka yanzu dole a ba wa yankin Kudu damar yin mulkin kasar a 2023,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa naa Twitter.

 

Dag Sagir Kano Saleh, Baba Martins (Abuja) da Hope Abah Emmanuel (Makurdi) da  Abiodun Alade (Legas)