✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Makarantun tsangaya na kwana za su dauki sabbin dalibai

Sabbin makarantun tsangaya na kwana guda uku da aka gina a Jihar Kano za su fara daukar sabbin dalibai nan ba da jimawa ba. Kwamishinan…

Sabbin makarantun tsangaya na kwana guda uku da aka gina a Jihar Kano za su fara daukar sabbin dalibai nan ba da jimawa ba.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Muhammad Sanusi Sa’id Kiru ya sanar da hakan lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatin jihar zuwa rangadin makarantun a ranar Talata.

Ya ce gwamnatin jihar za ba da fifiko wajen daukar almajiran da aka dawo da su daga wasu jihohi a makarantun da ta gina.

Kiru ya ce an gina makarantun ne a mazabun ‘Yan Majalisar Dattawa uku da ke jihar a kananan hukumomin Bunkure, Madobi da Bagwai  domin karawa a kan guda 12 da jihar ke da su baya.

“Mun gina karin makarantun ne guda uku saboda mu tabbatar da kokarin da Gwamnatin Jihar Kano ke yi wajen saka dukkanin almajiran da aka dawo mana da su jihar a cikinsu saboda su samu ilimin boko da na Muhammadiyya”, inji kwamishinan.

Dakin koyon kwamfuta a daya daga cikin makarantun

An yi wa sabbin makarantun kwanan gine-ginen ajujuwa, dakunan kwanan dalibai, masallatai, dakunan karatu, wutar lantarki da ma injinan samar da wutar lantarki saboda shirin ko-ta-kwana.

Kwamishinan ya ce an tsara makarantun ne ta yadda za su rika koyar da almajiran ilimin zamani da na addini, shi ya sa aka gina musu dakunan koyon kwamfuta da na gwaje-gwajen kimiyya.

Daya daga cikin ajujuwan makarantun

Ya ce tuni aka kusa kammala aiki a makaratun kafin a fara karatu gadangadan a cikinsu.

Da yake tsokaci yayin ziyarar da aka kai daya daga cikin makarantun da ke yankinsa, Shugaban Karamar Hukumar Bunkure, Rabi’u Bala Bunkure ya yaba wa gwamnatin jihar bisa kawo makarantar yankinsa.

Ya kuma yi alkawarin yin dukkannin mai yiwuwa wajen kulawa da makarantar.

Shi kuwa shugaban Hukumar Kula da Makarantun Allo da na Islamiyyah ta Jihar Kano, Gwani Yahuza Gwani Dan-Zarga cewa ya yi kowacce daga cikin sabbin makarantun na da karfin dibar dalibai 976 daga cikin wadanda aka dawo wa jihar da su daga wasu jihohi.

Ya kuma ce an samar da dukkanin kayyakin da ake bukata wajen bunkasa yanayin koyo da koyarwa a cikinsu.