Adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da COVID-19 a Najeriya ya haura 6,000 yayin da wadanda suka rasu a sanadiyar cutar suka doshi dari biyu.
Alkaluma na baya-bayan nan da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta wallafa a shafinta na Twitter sun nuna cewa mutum 6,175 ne jimillar wadanda gwaji ya nuna sun kamu, yayin da aka sallami mutum 1,644 bayan sun warke, 191 kuma suka riga mu gidan gaskiya.
Hukumar ta kuma kididdige sabbin majinyatan da aka samu a ko wacce jiha, kuma kididdigar ta nuna cewa 74 a jihar Legas suke.
A jihar kuma Katsina an samu mutum 33, yayin da aka samu 19 a Oyo, 17 a Kano, 13 a Edo, da kuma 10 a jihar Zamfara.
Sauran jihohin su ne Ogun da Gombe da Borno masu mutum takwas-takwas, sai Bauchi da Kwara masu bakwai-bakwai, da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya da ke da mutum hudu.
A jihohin Kaduna da Enugu an samu mutum uku-uku, sai jihar Ribas da ke da mutum biyu.
Jihar Legas ce dai ke da kaso mafi tsoka na wadanda suka kamu da mutum 2,624, sai jihar Kano na biye mata da 842, Yankin Babban Birnin Tarayya kuma na rufa musu baya da 422.