✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Musulunci ta yi wa CAN tatas kan nadin alkalai

Ya zama dole sabo CAN ta dade tana hayagaga da nuna tsananin kiyayyarta ga Musulunci

Majalisar Kolin Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta caccaki Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), bisa abin da Majalisar ta kira hayagagar CAN kan jerin sunayen alkalai 20 da za a nada a Kotun Daukaka Kara.

NSCIA ta ce ita ba ta son kula kungiyar, amma yin hakan a wannan kaorn ya zama jazaman, ganin yadda CAN din ta dade tana barin zance da nuna tsananin kiyayyarta ga Musulunci da Musulmai.

Ta ce, hayaniyar CAN din ne ya sa a kwanakin baya Majalisar fallasa yadda aya yi ta danne Musulmai wurin nada Kwamitin Amintattun Gidan Talabijin na Kasa (NTA) inda CAN din ke zargin an nuna wa Kiristoci bambanci.

Sanarwar da Mukaddashin Darakantan Gudanarwan NSCIA, Farfesa Salisu Shehu da Mataimakin Babban Sakatare, Arc. Haruna Zuberu Usman-Ugwu suka fitar ta ce, “Keta da zalunci ne zargin Musulmi da nuna wa wasu fifiko alhali su ne Kiristoci suke dannewa ta hanyoyi daban-daban,,” inji NSCIA.

Majalisar Kolin Harkokin Musuluncin ta ci gaba da cewa toshewar basira ce CAN ta zo tana maganar sunayen alkalai 20 da za a nada.

“Matsalar CAN da wasu masu riya cewa su ke fada a ji, suke hayaniya a kai shi ne saboda 13 daga cikin alkalai 20 da za a nada daga yankin Arewa Musulmai ne.

“Shugabar Kotun Daukaka Karara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta fada cewa an fitar da sunayen ne ta hanyar bin ‘ka’ida yadda aka saba’, aka kuma ba da shawara ‘ba tare da nuna wani fifiko na yare, addini ko kungiya ba’. Amma hakan bai hana taratsi da son zuciya na addini sukar lamarin ba.

“A kokarin bayyana adawarta, CAN da magoya bayanta sun ki lura da cewa Musulmi su ne mafiya karanci a Kotun Daukaka Kara.

“Alkalai 70 ne a Kotun Daukaka Kara, amma yankin Arewa mai jihohi 19, na da alkalai 34 daga cikinsu; Kudu mai jihohi 17 kuma na da alkalai  36. Wato Kudu ta fi Arewa yawan alkalai a Kotun.

“Cikin alkalai 36 daga yankin Kudu ma, a Kudu maso Yamma inda Musulumi ke da rinjaye, da Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma da kowannensu ke da Musulmi, daukacin alkalan Kiristoci ne face Mai Shari’a Habeeb Adewale Abiru daga Jihar Legas da Mai Shari’a Mistura Bolaji-Yusuf daga Jihar Oyo.

“A yankunan Arewa uku da Musulmi ke da rinjaye, alkalai 34 kuma 15 daga cikinsu Kiristoci ne: Arewa maso Gabas, Musulmi 4, Kiristoci 7; Arewa ta Tsakiya Musulmi 6, Kiristoci 7; Arwea maso Yamma kuma Musulmi 9 Kirista 1.”

Amma a Kudu gaba daya, Musulmi biyu ne kawai, su din ma yankin Kudu maso Yamma, amma a Arewa Kirisoci 15 ne.

“Saboda haka surutun CAN cewa an danne kiristoci tsabar karya ce da munafurci don ta rufe yadda ake fifita su a kan Musulmi.

“Addini na kira ne ga kaunar juna, gaskiya, amana da rungumar juna da kyautata makwabtaka, amma CAN ta yi nasarar dasa kiyayya da rashin amana da yaudara da mugunta,” inji sanarwar.