✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Katsina ta amince a kafa kwalejin noma a Daudawa

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta amince da kafa Kwalejin Harkokin Noma a garin Daudawa, Karamar Hukumar Faskari. Mataimakin Shugaban Majalisar, Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ne…

Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta amince da kafa Kwalejin Harkokin Noma a garin Daudawa, Karamar Hukumar Faskari.

Mataimakin Shugaban Majalisar, Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ne ya gabatar da kudurin a zauren majalisar.

Yayin gabatar da kudurin, Hon Tafoki mai wakilatar yankin ya ce, “Kuduri ne da ke fatan samar da cikakkiyar kwalejin harkokin noma da za ta yi gogayya da kowace kwaleji a ko’ina a fadin kasar nan”.

Dan majalisar ya ce, kudurin ya kuma kunshi daga darajar makarantar bayar da horo kan harkokin Noma da ke Daudawa zuwa matakin makarantar gaba da sakandire ta yadda zata rika bayar da shaidar karatu na Diploma da makamantansu a fannin Noma.