✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Kano ta amince Ganduje ya karbo bashin N20bn

Majalisar ta ce ta amince wa gwamnan jihar ciyo bashin 20bn ne duba da yadda tattalin arziki ya tabarbare.

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da bukatar Gwamna Abdullahi Ganduje na karbar rancen Naira biliyan 20 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) ta hannun Bankin United Bank for Africa (UBA).

A zamanta na ranar Litinin, Shugaban Majalisar, Abdulazeez Garba Gafasa, wanda ya karanta wasikar gwamnan, ya ce bashin kayayyakin aikin yana da kashi tara na kudin ruwa da za a biya cikin shekara 10.

Ya ce rancen zai dace da yunkurin jihar na sake fasalin tattalinta da annobar COVID-19 ta lalata.

Gwamna Ganduje a cikin wasikar, ya ce ya fada wa masu ruwa da tsaki cewa an samu sauyin tattalin arziki tun a shekara ta 2016.

Shugaban Masu Rinjaye, Kabiru Hassan Dashi, ya bukaci Majalisar ta yi la’akari da bukatar ta gwamnan, saboda kalubalen da kasuwar Kano ta samu sakamakon tabarbarewar yanayin tattalin arziki.

Ya ce an amince da rancen ne don cike gibin matsalar tattalin arziki da annobar COVID-19 ta haifar.

Bayan tattaunawa, Majalisar ta amince baki daya da bukatar.