✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta bukaci gwamnatin tarayya ta magance yunwa a Najeriya

Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta shirya magance farin abinci nan da wani lokaci.

Majalisar Wakilai ta bukaci Gwamnatin Tarayya  da TA yi gaggawar yin shiri don dakile matsalar karancin abinci da ta kunno kai a kasar nan.

Majalisar dai ta bukaci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da Fadar Shugaban Kasa da Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya da su yi abin da ya dace don magance kalubalen.

Majalisar ta kuma umarci dukkan kwamitocinta masu alaka da aikin gona da su tuntubi ma’aikatu da hukumomin da suka dace da kuma abokan huldar kasa da kasa don fara aiwatar da sarrafa albarkatun abinci da kuma dakile matsalar karancin abinci a kasar.

Kudurin ya biyo bayan amincewa da kudirin da Rimamnde Shawulu da Solomon Bob suka yi.

Shawulu, yayin da yake gabatar da kudurin ya ce, duniya gaba daya na cikin fargabar fuskantar karancin abinci wanda ke da alaka da yakin Ukraine da Rasha.

Dan majalisar ya ce wani rahoto da Babban Bankin Najeriya (CBN), ya fitar a baya-bayan nan ya nuna cewa kudin shigo da abinci a Najeriya ya karu da kashi 45 zuwa Dala biliyan 2.71 cikin wata 12 a 2021.

Ya kara da cewa, a yayin da ake fama da kalubalen tsaro a fadin kasar nan, karancin abinci da kuma matsaloli sun karu zuwa wasu jihohi da dama tare da hasashen cewa akalla jihohi 16 za su fuskanci matsalar karancin abinci.

Ya ce matsalar ta kara ta’azzara inda ‘yan ta’adda suka yi wa gonaki kawanya, suna garkuwa da manoma, sannan suna tilasta mazauna kauyuka da manoma biyan kudin fansa ko wasu kudade kafin su shiga gonakinsu.