✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta amince Tinubu ya nada hadimai 20

Sai dai Tinubu bai bayyana sunayen wadanda zai bai wa mukaman ba.

Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Shugaban Kasa Bola Tinubu ta nada masu ba shi shawara na musamman guda 20.

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar Tinubu a zauren majalisar a ranar Talata.

Sai dai a cikin wasikar da aka aike wa Majalisar Dattawan, shugaban kasar bai bayyana sunayen masu ba da shawara na musamman guda 20 ba da zai nada ba.

Amma bayan karanta wasikar, babban zauren majalisar ya amince da bukatar cikin gaggawa.