✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maikyau ya zama sabon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa

Maikyau ya shugaban kungiyar na 36.

Babban Lauyan Najeriya (SAN), Mista Yakubu Chonoko Maikyau ya zama sabon shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa (NBA).

A yanzu Maikyau shi ne na 36 jerin shugabannin kungiyar, inda kada masa kuri’a yayin zaben da aka gudanar ta Intanet a ranar Asabar.

Ya samu kuri’a 22,342 inda ya doke wasu ‘yan takara biyu, Messrs Joe-Kyari Gadzama (SAN), Shugaban Kwamitin Hulda da Hukumomin Tsaro na NBA; da kuma Jonathan Taidi, tsohon Babban Sakatare na NBA.

A cewar shugaban kwamitin zaben NBA, Mista Ayodele Akintunde (SAN), mutum 59, 392 ne suka yi rajistar katin zaben, sannan mutum 3000 ba su damar kada kuri’a ba sakamakon gaza tantance bayanansu.

Ya ce Maikyau ya samu kuri’a 22,342 wanda ya yi daidai da kashi 64.6 cikin 100 na kuri’un da aka kada, yayin da Gadzama ya samu kuri’a 10,842, shi kuma Taidi ya samu kuri’a 1,380.

Sauran wadanda suka lashe gurabe a zaben sun hada Misis Linda Bala (Mataimakiya ta farko), Clement Ugo (Mataimaki na biyu), Misis Amanda Demechi Asagba (Mataimakiya ta uku).

Sauran su ne Adesina Adegbite (Babban Sakatare), Daniel Kip (Mataimakin Babban Sakatare), Misis Caroline Anze-Bishop (Ma’aji), Misi Chinyere Obasi (Sakataren Walwala), Habeeb Lawal (Sakatare Yada Labarai) sai kuma Charles Ajiboye (Mataimakin Sakataren Yada Labarai).