✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maidakin Sarkin Daura ta rasu  

Da safiyar yau Juma’a ne aka sanar da rasuwar maidakin Sarkin Daura Hajiya Binta Lolo Umar Farouk. Hajiya Binta ta rasu tana da shekara 70…

Da safiyar yau Juma’a ne aka sanar da rasuwar maidakin Sarkin Daura Hajiya Binta Lolo Umar Farouk.

Hajiya Binta ta rasu tana da shekara 70 ta kwashe shekara tara tana jinya. Kamar yadda Sarkin Labarai Usman Ibrahim ya shaidawa  Aminiya,

Marigayiyar ta rasu ta bar ‘ya’ya shida, biyu maza, hudu mata.

Daga cikin mazan akwai Danburan Daura Hakimin Baure Alhaji Daha Muhammad Umar Farouk.

Kamar yadda Aminiya ta samu rahoton, Hajiya Binta tayi fama da ciwon hawan jini, ciwon suga da kuma na kafafu.

Tuni dai aka yi jana’ izarta a makabartar Gabas, yayin da Malam Salisu Rabi’u ya jagorancin sallar gawar.