Hukumar Tsaro ta Cibil Defence a Jihar Nasarawa ta kama wani tsoho mai shekara 75 mai suna Ali Isah bisa zarginsa da laifin yin fyade ga wata ’yar makwabtansa mai shekara 3.
Kwamandan Hukumar Muhammad Mahmoud Fari ya ce jami’ansa sun kama wanda ake zargin ne a kauyen Kandere da ke Kokona a Karamar Hukumar Kokona bayan wadansu mazauna kauyen sun sanar da su lamarin. Ya ce a halin yanzu jami’ansa suna ci gaba da gudanar da bincike a kan wanda ya ake zargin kuma da zarar sun kammala za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Wanda ake zargin Ali Isah bai musanta zargin da ake yi masa ba sai dai ya alakanta lamarin ga aikin Shaidan.
Wakilinmu ya gano cewa wanda ake zargin magidanci ne da yake da mata biyu da ’ya’ya 11.