✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mai neman takarar Shugaban Kasa a NNPP ya janye wa Kwankwaso

Dan siyasar ya janye takararsa tare sa mara wa Sanata Kwankwaso baya

Wani mai neman takarar Shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP, Olufemi Ajadi Oguntoyin, ya janye daga takararsa, inda ya goyi bayan jagoran jam’iyyar na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Da ya ke jawabi a wani taron da aka gudanar a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun a ranar Alhamis, Oguntoyin, ya ce ya janye takararsa ne domin mara wa tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabiu Kwankwaso baya a takarar ta Shugaban Kasa.

“Ni Olufemi Ajadi Oguntoyinbo, bayan da na yi la’akari da abubuwa da yawa, kuma bisa maslahar babbar jam’iyyarmu da kasarmu, a yau na janye burina na tsayawa takarar Shugaban Kasa na goyi bayan takarar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

“Na yi alkawarin yin biyayya a kowane lokaci don yin hidima ga jam’iyyarmu da kasarmu,” inji shi.

Jam’iyyar NNPP dai na ci gaba da samun tagomashi, inda ’yan siyasa ke sauya sheka zuwa cikinta.