✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun sace basarake a Kogi

Kakakin ’yan sandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.

An yi garkuwa da basaraken Oghara da ke Karamar Hukumar Kabba Bunu a Jihar Kogi.

Wasu ’yan bindiga ne suka kai farmaki fadarsa da sanyin safiyar ranar Talata suka yi awon gaba da shi.

An ruwaito cewa maharan sun harbe wata ma’aikaciyar fadar mai suna Toyin Onare a yayin harin.

Haka kuma sun yi garkuwa da wasu hakimai biyu; David Obadofin da Temidayo Elewa.

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kogi, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ’yan ta’addan sun isa fadar ne da misalin karfe 3 na dare, suka yi ta harbe-harbe.

Aya ya kara da cewa Cif Obadofin wanda babban manomi ne kuma basaraken gargajiya tare da daya daga cikin yaransa na hutawa a kofar gidansa lokacin da aka kai harin.

Ya ce ’yan bindigar sun yi awon gaba da basaraken da Temidayo zuwa daji, sai dai ya ce mutum daya ya tsere.

Ya ce Toyin, wanda aka harba a fadar ya rasu a Babban Asibitin Kabba da ke hedikwatar karamar hukumar.

SP Aya ya kara da cewa kwamishinan ’yan sandan jihar, Hakeem Yusuf, ya tura jami’an rundubar dabaru ta musamman zuwa yankin domin bankado wadanda suka kai harin tare da ceto basaraken.