✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahara sun kashe sojoji sun kona sansaninsu a Neja

Soja biyar da wasu mutum biyu sun rasu sannan aka sace mutum 15

Sojoji biyar da wasu mutum biyu sun kwanta dama a harin ’yan bindiga da suka kuma yi garkuwa da mutum 15 a Jihar Neja.

Maharan sun shammaci wani jami’an tsaron hadin gwiwar sojoji, ’yan sanda, ‘sibil difens’ da ’yan banga da ke yankin Allawa, suka kashe soja biyar da dan ‘sibil difens’ daya, suka kona sansanin da motocin, wasu jami’an tsaron kuma suka tsira da raunukan harbi.

Shugaban Matasan Shiroro, Mohammed Sani Idris, ya ce maharan su kusan 100 sun yi kusan awa biyar suna barna a yankunan Allawa, Manta, Gurmana, Bassa da Kokki a karamar Hukumar.

“Sun kashe wani mai suna Alhaji Sale a unguwar Madalla da ke yankin Bassa suka kuma sace wasu mutum hudu da babura biyu.

“A Kokki Boddo kuma an sace mutum shida da babura biyar, sannan a Manta an sace mutum biyar,” inji shi.

Sanan kuma suka kona motar sojoji a hare-haren tsakanin ranar Laraba zuwa safiyar Alhamis.

Mohammed, ya yi roko ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Neja da su kara zage damtse wajen kare rayukan jama’a.