✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahara sun kashe lauya sun tafi da iyalansa

Bayan sun hahharbe shi sannan suka yi awon gaba da iyalansa

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne, sun hallaka wani lauya, suka kuma yi garkuwa ta matarsa da dansa a Kaduna.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun shiga gidan lauyan mai suna Haro Gandu inda suka kashe shi su kayi garkuwa da mai dakinsa da dansa.

Masu garkuwa da mutanen sun kutsa cikin gidan marigayin da ke yankin Tolgate a kan hanyar Abuja daga Kaduna ne bayan sun fasa tagar gidan.

Dan uwan mamacin, Timothy Gandu wanda tsohon kwamishina ne a Jihar Kaduna ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce ‘yan bindigar sun harbi dan uwansa a kafa da ta baya a lokacin da ya yi yunkurin tsere masu.

Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun tafi da matar dan uwansa da dansa.