✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifin Shaikh Auwal Albani ya rasu

Allah Ya yi wa mahaifin marigayi Shaikh Muhammad Awwal Adam Albani Zariya rasuwa.

Allah Ya yi wa mahaifin sahararren malamin Musulunci marigayi Shaikh Muhammad Auwal Adam Albani Zariya rasuwa.

Da sanyin safiyar Laraba 18 ga watan Nuwamba 2020 ne Malam Adam Danjuma Tela ya rasu bayan fama da jinya aka kuma yi sallar jana’izarsa da safiya a gidansa da ke unguwar Mucjiya, Sabon Garin Zariya.

Da take sanar da rasuwar, Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS), ta ce, “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.

“Allah ya yi wa mahaifin marigayi Albani Zaria rasuwa a safiyar Larabar nan, mai suna Malam Adamu.

“Marigayin ya rasu kusan sallar asuba bayan ya yi fama da jinya, tuni aka yi sallar jana’izarsa a gidansa da ke ‘Yan Awaki, Muchiya, Sabon Garin Zaria”, inji Babban Sakataren JIBWIS na Kasa, Shaikh Muhammad Kabir Haruna Gombe.

Marigayi Malam Adamu Danjuma, mahaifain marigayi Shaikh Muhammad Auwal Adam Albani

Ta’aziyyar mahaifin Shaikh Albani

Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zaman, Isa Ali Pantami daya daga cikin makusantan Shaikh Albani, ya yi ta’aziyyar rasuwar Malam Adamu a shafinsa na Facebook.

“Inna lil Lahi wa inna ilaiHi Raji’un! Allah Ya jikan mahaifin marigayi Shaykh Muhammad Auwal Adam Albani Zariya, Wato Malam Adamu.

“Yau [Laraba] Allah Ya dauki rayuwarsa; Allah Ya jikan dukkan iyayenmu da malamanmu, sannan Ya kyautata namu bayan na su,…”