✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magidanci ya rataye kansa bayan ya harbe matarsa

Bayan da mijin ya ga mutane sun cika gidan sai ya tsere ya gudu daji ya je ya rataye kansa shi ma ya mutu.

Wani magidanci mai suna Akpan Asim ya kashe matarsa, Jannet Udom, sakamakon zarginta da yake yi cewa tana bin maza suna fasikanci.

Wannan lamari ya faru ne a kauyen Bashua a Karamar Hukumar Boki da ke Jihar Kuros Riba.

Majiyarmu ta ce Asim, ya kama matarsa ce a dakinsa da wani namiji suna badala, sai bai yi wata-wata ba ya dauko bindiga ya harbe ta bayan kwarton ya arce.

Wani makwabcinsu mai suna Solomon Osim ya shaida wa Aminiya cewa, “Koda Akpan ya shiga gida ya nufi dakinsa sai ya iske matar suna badala a kan gadonsu, sai kwarton ya tsere, yayin da mijin ya dauko bindigar farauta ya harbi matar sau uku inda ta mutu,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Bayan da mu makwabtaka muka ji karar harbin bindiga a gidan, sai muka halarci wajen don sanin me ke faruwa, muka tarar da matar kwance cikin jini rai ya yi halinsa.”

Ya kara da cewa, “Bayan da mijin ya ga mutane sun cika gidan sai ya tsere ya gudu daji ya je ya rataye kansa shi ma ya mutu.”

Bisa al’adar kabilar yankin, abin kunya ne wani ya rataye kansa. “Lokacin da wadansu mafarauta suka ga mutum ya rataye kansa a bishiya, sai suka sanar wa basaraken kauyen, shi kuma ya bayar da umarnin a binne shi a karkashin bishiyar.

Wakilinmu ya tuntubi DSP Irene Ugbo, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, wadda ta tabbatar da aukuwar lamarin amma ba ta yi  karin bayani ba.