✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magidanci ya fara tattaki daga Gombe zuwa Abuja saboda Tinubu/Shettima

Ya fara tattakin kilomita 425 domin gayyato Shettima zuwa Gombe

Wani magidanci mai ’ya’ya uku ya fara tattaki daga Gombe zuwa Abuja don nuna kaunarsa bisa yadda dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya zabi Kashim Shettima ya zama abokin takararsa a shekarar 2023.

Magidancin mai suna Muhammad Umar, ya fara tafiyar tasa mai tsawon kilomita 425 ne, yana kyautata zaton isa Abuja cikin kwanaki 10.

Matashin wanda dan Karamar Hukumar Balanga ta Jihar Gombe ne, shi ne Kodinetan Arewa maso Gabas na Kungiyar Magoya Bayan Tinubu da Shettima mai suna TINKAS.

Ya ce zai yi tattakin ne zuwa Abuja domin ya gayyato Kashim Shettima ya zo ya kaddamar musu da ofishinsu na shiyar da ke Gombe.

Ya ce shi da magoya bayansa, burin su a 2023 Bola Tinubu da Kashim Shettima su lashe zaben shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyarsu ta APC.

A cewarsa, “Zan yi Tattakin nan ne saboda ina kaunar Kashim Shettima kuma sai ga shi Bola Tinubu ya dauke shi mataimakin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyarmu ta APC wanda nake da tabbas zai dinke mana yankinmu waje guda,” in ji Umar.

Umar ya ce kafin fara wannan tattakin, iyalan sa sun yi masa fatan alheri da addu’ar Allah Ya tsare masa hanya, inda ya ce ya shirya tsaf hatta wasu ’yan magunguna ya tanada saboda karamar jinya.

Daga nan ya ce a lokacin tattakin, idan ya yi dare zai gabatar da kansa ga jami’an tsaro don ya samu wajen kwana a wajensu da safe ya ci gaba da tafiya.

Mambobin kungiyar ta Tinkas da sauran abokan arziki sun masa bankwana da fatan alheri kafin ya kama hanya