Wasu mafarauta a unguwar Ruga da ke Ƙaramar hukumar Mafa a Jihar Borno, sun yi nasarar ƙwato shanu 10 da ’yan Boko Haram da ISWAP suka sace.
Rahoton rundunar ’yan sandan jihar daga Kakakin ‘yan sandar Nahum Daso ne ya bayyana cewa, mafarautan sun samu labari daga wasu manoma cewa ’yan ta’adda sun wuce zuwa dajin kusa da unguwar Ruga ɗauke da makamai da kuma shanu.
- Jama’a na neman ɗauki kan ƙwacewar mesa daga gidan Tsohon Akanta-Janar a Kano
- Buhari bai taɓa girmama kowa kamar yadda Tinubu ya yi masa ba — Sani
Ɗaya daga cikin mafarautan ya ce sun haɗu gaba ɗaya, sannan suka kai wa ‘yan ta’addan farmaki a ranar 16 ga watan Yuli, 2025.
Ya ce, “Da muka hango su ɗauke da shanun da suk sace, sai muka farmake su da makamai. Sun gudu da wasu shanun amma mun samu nasarar ƙwato guda 10.”
An tafi da shanun da aka ƙwato don a adana su yayin da ake ci gaba da neman sauran dabbobin da kuma ‘yan ta’addan da suka tsere.
‘Yan sanda sun ce za su miƙa shanun da aka samu zuwa hukumar kula da kiwon dabbobi ta Jihar Borno (BORMA) bayan kammala bincike.