✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid da Gwamnatin Ribas sun kulla yarjejeniyar ci gaban wasanni

Madrid da Gwamnatin Jihar Ribas za su inganta wasanni tsakanin yara da matasa

Real Madrid da Gwamnatin Jihar Ribas sun rattaba hannu kan yarjejeniyar hadin kai don inganta wasanni tsakanin yara da matasa a Kwalejin Real Madrid da ke Fatakwal.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kelvin Ebiri, Mataimaki na Musamman kan harkokin Yada Labarai ga Gwamnan Jihar Ribas.

Kamar yadda Gidan Rediyon Faransa RFI ya ruwaito, sanya hannu kan wannan yarjejeniya ya gudana ne tun a watan Oktoban da ya gabata a dakin taro na Real Madrid Sport City, da ke Madrid na Spain.

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, a madadin Gwamnatin Jihar Ribas da Mista Enrique Sanchez, Mataimakin Shugaban Zartarwa, Gidauniyar Real Madrid da Mista Jihad Saade, Shugaba, Interact Sports, ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.